Kungiya Ta Bulla a Kano, Ana Son Abba Ya Bijirewa Kwankwaso Kafin Tafiya Tayi Nisa

Kungiya Ta Bulla a Kano, Ana Son Abba Ya Bijirewa Kwankwaso Kafin Tafiya Tayi Nisa

  • Wasu ‘yan siyasa daga jam’iyyu dabam-dabam sun fara kira ga Abba Kabir Yusuf ya tsaya a kan kafafunsa da kyau
  • Masu wannan raji sun kira kungiyarsu da Abba tsaya da kafanka da nufin ceto Kano daga hannun Rabiu Kwankwaso
  • Sani Makale Kura Mai tafiyar sa’a ya zargi Kwankwaso da yin kane-kane da hana Abba Gida Gida yin aikinsa da kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - A halin yanzu ana ganin wani sauyi a jihar Kano, an samu masu kira ga Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafafunsa biyu.

Wata kungiya ta fito ta na mai neman gwamna Abba Kabir Yusuf ya daina biyayya ga kowa wajen juya madafun ikon Kano.

Kwankwaso Abba Kabir
Kungiya ta na zuga Abba Kabir Yusuf ya saba Rabiu Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tafiyar Abba Tsaya da kafanka a Kano

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

Rahotannin da aka samu daga tashar rediyon Freedom sun nuna an fito da wata kungiya mai suna ‘Abba Tsaya da kafanka’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ‘yan kungiyar nan su ke so shi ne mai girma gwamnan Kano ya jefar da rigar Kwankwasiyya wajen tafiyar da mulkinsa.

An zargi Kwankwaso da juya gwamnatin Abba

Masu wannan tafiya su na zargin cewa tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya zama karfen kafa, ya hana gwamna yin aiki.

A cewarsu, Madugun darikar Kwankwasiyyar ne yake juya ragamar mulki ba Abba Yusuf da al’umma suka zaba a zaben 2023 ba.

Alhaji Sani Makale Kura Mai tafiyar sa’a wanda ‘dan jam’iyyar APC ne, shi ne jagoran wannan tafiya da sunan nemawa jihar ‘yanci.

Sani Makale Kura Mai tafiyar sa’a ya zargi wasu kwamishinonin da yin biyayya ga Kwankwaso a maimakon gwamnan na Kano.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

Shi da ire-irensa sun ce bai kamata tsohon gwamnan ya rika tsoma baki ba, kyau ya maida hankalinsa a siyasar kasa gaba daya.

Jagororin tafiyar sun yi ikirarin cewa ba su da burin siyasa, illa iyaka a ceci jihar Kano daga halin da ta samu kanta a yanzu.

'Yan Kwankwasiyya sun yi kira ga Abba

Wasu mabiya Kwankwasiyya kuwa sun fara maida martani, su na jan kunnen gwamna Abba ya guji butulcewa ubangidan nasa.

Masoyan Kwankwaso sun zargi makiya da shirya aikin, suka ce haka aka zuga Salihu Takai ya juyawa Ibrahim Shekarau baya.

"Abba yana kan kafarsa" - NNPP

Shugaban NNPP na Kano, Hashim Dunguruwa ya shaidawa gidan rediyon cewa dama can Abba a kan kafafunsa yake ban a kowa ba.

Dunguruwa ya ce gwamna Abba Gida Gida yana tafiye ne a kan kafarsa daram kuma babu wanda yake juya masa akalar mulki.

Kawun gwamna Abba zai samu sarauta

Kara karanta wannan

Gobara: Gwamna ya cika alkawari, Abba ya ba yan kasuwa tallafin N100m

Ana da rahoto cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi II zai nada Alhaji Abba Yusuf a matsayin sabon Danmakwayon Kano a watan nan.

Kakan gwamnan Kano, Alhaji Yusuf Bashari ya rike wannan sarauta kafin ya rasu a shekarar 1965, tun lokacin ba su sake sarauta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng