Ana Tsaka da Rigimar PDP, Jam'iyyar APC ta Dakatar da Ministan Tinubu da Jiga Jiganta

Ana Tsaka da Rigimar PDP, Jam'iyyar APC ta Dakatar da Ministan Tinubu da Jiga Jiganta

  • Jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta tabbatar da dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri a yau Juma'a
  • Jam'iyyar ta kuma dakatar da dan takarar gwamna a zaben 2019, David Lyon da wasu kwamishinoni a gwamnatin PDP
  • Wannan na zuwa ne bayan tsagin jam'iyyar PDP ya dakatar da Umar Damagun daga mukaminsa a yau Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta sanar da dakatar da Minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Jam'iyyar APC ta reshen kananan hukumomin Ekeremor da Southern Ijaw sun sanar da dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri.

APC ta dakatar da Minista a gwamnatin Tinubu
Jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta dakatar da ƙaramin Ministan mai, Heineken Lokpobiri. Hoto: Heineken Lokpobiri.
Asali: Getty Images

APC ta dakatar da manyanta a Bayelsa

Kara karanta wannan

Damagum: Kotu ta dakile kwamitin gudanarwar PDP, ta ba da sabon umarni

Channels TV ta ruwaito cewa APC ta kuma dakatar da dan takarar APC a zaben gwamna a 2019, David Lyon daga jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, daga cikin wadanda aka dakatar akwai kwamishinoni da ke riƙe da mukami a gwamnatin PDP ta Douye Diri.

Shugaban jam'iyyar a karamar hukumar Ekeremor, Mitin Eniekenemi ya ce sun dakatar da karamin Minista, Heineken Lokpobiri.

Eniekenemi ya kuma tabbatar da dakatar da kwamishinan makamashi a jihar, Injiniya Karin Kumoko.

Musabbabin dakatar da Ministan da jiga-jigan APC

Ana zargin dakatar da Ministan ne da sauran jiga-jigan jam'iyyar kan yi mata zangon-kasa da kuma barka ta gida biyu.

Yayin da yake zantawa da yan jaridu, Eniekenemi ya ce sun dauki matakin ne duba da sashe na 21 cikin kundin tsarin jam'iyyar APC.

Bayan haka, jam'iyyar APC a karamar hukumar Southern Ijaw ta dakatar da kwamishina a gwamnatin Douye Diri da wasu jiga-jiganta guda shida.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

PDP ta dakatar da shugabanta, Umar Damagum

Kun ji cewa tsagin PDP ya dakatar da shugaban jam'iyyar ta kasa, Umar Damagum daga mukaminsa a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.

Dakatarwar na zuwa ne bayan kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin Damagum ya dakatar da wasu jiga-jigan PDP.

Daga bisani, tsagin jam'iyyar ya nada sabon mukaddashin shugabanta na kasa, Ahmed Mohammed Yayari domin jagorantarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.