Atiku Ya Amince Gwamnan Bauchi Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP a 2027?

Atiku Ya Amince Gwamnan Bauchi Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP a 2027?

  • Jam'iyyun adawa na ci gaba da wasa wukakensu domin tube Bola Tinubu daga kan kujerar shugaban kasa a zaben 2027
  • Wani dan soshiyal midiya ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya amince gwamnan Bauchi ya zama dan takarar PDP
  • An gudanar da binciken kwa-kwaf kan wannan ikirari kuma gaskiya ta bayyana kan matsayar da aka ce Atiku ya dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tuni dai jam'iyyun adawa suka fara shirye-shiryen zaben shugaban Najeriya na 2027 bayan watanni 18 da hawan rantsar da shugaba Bola Tinubu.

Ana ta yada jita-jita game da yiwuwar kawance tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da Peter Obi na jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

An gano gaskiya kan ikirarin Atiku ya amince gwamnan Bauchi ya zama dan takarar PDP a 2027
Atiku bai amincewa gwamnan Bauchi ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP a 2027 ba. Hoto: @mahbeel_A
Asali: Twitter

An ce Atiku ya hakura da takara

A kwanan nan ne wani dan soshiyal midiya ya wallafa a shafinsa na X cewa Atiku Abubakar hakura da yin takarar shugaban kasa a zaben na 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawallafin ya ce Atiku da kansa ya amince da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben.

Sai dai binciken kwa-kwaf da shafin Dubawa ya yi ya nuna cewa hotunan da d'an soshiyal midiyan ya yi amfani da su ba na yanzu ba ne.

Atiku ya magantu kan takarar 2027

Binciken ya nuna cewa an dauke su tun wata ziyarar ban girma da Gwamna Mohammed da masu ruwa da tsaki na PDP suka kai wa Abubakar a shekarar 2022.

Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku ya karyata wannan ikirari, inda ya ce yanzu Atiku ya mayar da hankali ne wajen warware rigingimun PDP ba zaben ‘yan takara ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan rahoton da aka kirkire su domin cimma wata manufa, yana mai jaddada cewa Atiku bai furta irin wannan magana ba.

Abin da bincike ya nuna

Maganar cewa Atiku Abubakar da jiga jigan jam’iyyar PDP sun amince su tsayar da Gwamna Mohammed a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2027 karya ne.

Hotunan da aka wallafa domin nuna cewa ikirarin gaskiya ne an dauke su tare da wallafa su tun a shekarar 2022.

Uwa uba kuma, a zantawar da aka yi da mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasar, Paul Ibe, ya ce ko dan Atiku bai fadi makamanciyar wannan magana ba.

Duba abin da d'an soshiyal midiyan ya wallafa a kasa:

Atiku zai samu tikitin takara a PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa kakakin kungiyar matasan PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya ce Atiku Abubakar zai iya samun tikitin takara a 2027.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Sai dai Glintstone ya ce Atiku ba zai samu tikitin takarar 'haka kurum' ba, a cewarsa dole sai tsohon mataimakin shugaban kasar ya gwabza da sauran 'yan takara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.