Rikicin PDP Ya Sake Dagulewa, an Nada Sabon Shugaban Jam'iyyar, Bayanai Sun Fito

Rikicin PDP Ya Sake Dagulewa, an Nada Sabon Shugaban Jam'iyyar, Bayanai Sun Fito

  • Rikicin jam'iyyar PDP ya sauya salo bayan nadin mukaddashin shugaban jam'iyyar ta kasa a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024
  • Tsagin PDP a Najeriya ya nada Ahmed Yayari Mohammed a matsayin mukaddashin shugabanta bayan dakatar da Umar Damagun
  • Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta tsunduma cikin rikici yayin da aka fara shirye-shirye kan zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsagin jam'iyyar PDP a Najeriya ta amince da zaben mukaddashin shugbanta a Abuja.

Jam'iyyar ta zabi Ahmed Mohammed Yayari a matsayin wanda zai jagorance ta na wucin-gadi kafin ɗaukar matakin gaba.

PDP ta nada sabon mukaddashin shugabanta na kasa
Tsagin jam'iyyar PDP ta nada sabon mukaddashin shugabanta a Najeriya. Hoto: Peoples Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

An nada Yayari ya zama shugaban PDP

Kara karanta wannan

Damagum: Kotu ta dakile kwamitin gudanarwar PDP, ta ba da sabon umarni

Punch ta ce hakan ya biyo bayan dakatar da shugaban PDP, Umar Damagun da aka yi a birnin Tarayya, Abuja a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin nadinsa, Ahmed Yayari ya rike mukamin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Gombe, Channels TV ta ruwaito.

Yayari ya rike muƙamin ne daga shekarar 2011 zuwa 2019 a zamanin mulkin tsohon gwamna, Ibrahim Hassan Dankwambo.

An dakatar da wasu jiga-jigan PDP na kasa

Da safiyar yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024, kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin Umar Damagun ya dakatar da wasu jiga-jigan PDP.

Yayin zaman, an dakatar da sakataren yada labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba da mai ba ta shawara kan shari'a, Kamaldeen Ajibade.

Jim kaɗan bayan daukar matakin, tsagin jam'iyyar ya dakatar shugabannta, Umar Damagun da sakatarenta, Sam Anyanwu.

PDP ta lashe zaben kananan hukumomin Plateau

Kara karanta wannan

PDP ta sake rikicewa, an dakatar da wasu manyan jami'an jam'iyyar na kasa

Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Filato ta fara bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar.

A jiya Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024, shugaban hukumar, Plangji Cishak ya ayyana PDP a matsayin wanda ta lashe kananan hukumomi 10 a zaben.

Shugaban hukumar ya ce akwai sauran kananan hukumomin da ba a kai ga bayyana sakamakon zaben nasu ba, wanda a yanzu kowa yake jira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.