PDP Ta Sake Rikicewa, An Dakatar da Wasu Manyan Jami'an Jam'iyyar na Kasa

PDP Ta Sake Rikicewa, An Dakatar da Wasu Manyan Jami'an Jam'iyyar na Kasa

  • 'Yan mintoci kadan bayan sanar da dakatar da shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, jam'iyyar ta dakatar da wasu shugabanni
  • A cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran PDP na kasa, Chinwe Nnorom ya fitar, jam'iyyar ta dakatar da satarenta na yada labarai
  • Hakazalika, PDP ta dakatar da babban lauyanta da ke ba ta shawara kan harkokin shari'a, tare da bayyana wadanda za su maye gurbinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sabuwar matsala ta kunno kai yayin da kwamitin ayyuka na PDP na kasa ya sanar da cewa ya dakatar da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba.

An rahoto cewa kwamitin gudanarwa ya kuma dakatar da babban lauyan da ke ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a, Kamaldeen Ajibade, SAN.

Kara karanta wannan

Sanata Buba da aka alakanta da 'yan bindiga zai fito takarar gwamnan Bauchi?

PDP ta sanar da dakatar da wasu manyan jami'anta na kasa guda biyu
PDP ta dakatar da sakataren yada labarai da babban mai ba ta shawara kan harkokin shari'a. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Daraktan yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Chinwe Nnorom ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Juma’a, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta dakatar da manyan jami'anta

Chinwe Nnorom ya bayyana cewa jam'iyyar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban PDP na kasa (Kudu), Taofeek Arapaja.

A cewarsa, kwamitin zai gudanar da bincike kan korafe korafen da aka shigar kan manyan jami'an jam'iyyar bisa tsarin dokar da ta kafa PDP.

Sanarwar ta ce:

"A taronta na ranar Alhamis, 10 ga Oktobar 2024, kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya dakatar da Hon Debo Ologunagba da Kamaldeen Adeyemi Ajibade, SAN."

Me zai faru bayan dakatar da jami'an PDP?

Kafin a kammala binciken zarge zargen sabawa dokokin jam'iyyar da ake zargin manyan jami'an biyu sun aikata, Nnorom ya yi bayani kan wadanda za su maye gurbinsu.

Kara karanta wannan

Rigima ta koma sabuwa: An dakatar da shugaban PDP na kasa da sakataren jam'iyyar

Sanarwar ta ce:

“Bayan hukuncin da kwamitin ayyukan ya yanke, ya umurci mataimakan su (DNPS da DNLA) da su maye gurbinsu tare da kama aiki daga ranar Juma’a, 11 ga Oktoba, 2014.
“Ibrahim Abdullahi Manga, zai zama mukaddashin sakataren yada labarai na kasa da sai kuma Okechukwu Osuoha zai zama babban lauya mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a."

Kwamitin ayyukan ya umurci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki, jiga-jigai da magoya bayan babbar jam'iyyar da su ci gaba da harkokinsu yayin da PDP ke kula da komai.

PDP ta dakatar da Umar Damagum

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani tsagin kwamitin gudanarwa na PDP ya dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasala Umar Illiyasu Damagum.

Hakazalika, kwamitin ya dakatar da babban sakataren jam'iyyar na kasa, Samuel Anyanwu tare da mika su ga kwamitin ladabtarwa domin yin bincike a kan laifuffukansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.