Rigima Ta Koma Sabuwa: An Dakatar da Shugaban PDP na Kasa da Sakataren Jam'iyyar

Rigima Ta Koma Sabuwa: An Dakatar da Shugaban PDP na Kasa da Sakataren Jam'iyyar

  • Rigima ta koma sabuwa yayin da jam'iyyar PDP ta dakatar da shugabanta na kasa, Umar Damagum da kuma sakatarenta, Samuel Anyanwu
  • Wani tsakin kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa ne ya sanar da dakatar da Damagum da Anyanwu a safiyar ranar Juma'a, 11 ga Oktoba
  • Sanarwar da sakataren watsa labaran jam'iyyar Debo Ologunagba ya fitar ta ce an haramtawa Damagum da Anyanwu halartar tarurrukan PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rikicin cikin gida ya ki ci ya ki cinyewa a jam'iyyar adawa ta PDP, wani tsagin kwamitin ayyuka na kasa ya dakatar da shugaba da sakatare.

Tsagin ya dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Damagum da kuma sataren jam'iyyar na kasa, Samuel Anyanwu.

Kara karanta wannan

PDP ta sake rikicewa, an dakatar da wasu manyan jami'an jam'iyyar na kasa

PDP ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Umar Damagum
PDP ta dakatar da shugaban jam'iyyar da sakatare na kasa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Damagum: PDP ta dakatar da shugabanta

Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsagin kwamitin gudanarwa ya dakatar da shugaban da sakataren ne saboda kin yin biyayya ga jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Juma'a, ya sanar da dakatar da Damagum da Anyanwu.

Sanarwar ta ce:

"Kwamitin gudanarwan DP na kasa ya samu korafe korafe a kan mukaddashin shugaba, Ambasada Illiya Damagum da sakatare na kasa, Sanata Samuel Anyanwu."

Dalilin dakatar da Damagum, Anyanwu a PDP

Debo Ologunagba ya yi karin haske kan laifuffukan da ake zargin Damagum da Anyanwu sun aikata da ya jawo aka dakatar da su yana mai cewa:

"Kwamitin NWC ya dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa da sakatare na kasa saboda cin mutuncin dokar da ta kafa PDP da kuma karya alkawuran da suka dauka na aiki.

Kara karanta wannan

Damagum: Guguwar adawa na shirin kifar da shugaban PDP, ana shirya makarkashiya

"Bisa ga sashe na 57, 58, da 59 na dokar PDP, an dakatar da Ambasada Illiya Damagum da Sanata Samuel Anyanwu kuma an mika su ga kwamitin ladabtarwa na kasa domin bincike."

Sanarwar ta ce manyan shugabannin jam'iyyar ba za su sake halartar tarurruka ba ko yin wasu shirye shirye a madadin jam'iyyarhar sai kwamitin ladabtarwa ya kammala bincike.

PDP ta dakatar da manyan jami'ai

A wani labarin, mun ruwaito cewa PDP ta dakatar da sakatarenta na yada labarai na kasa, Debo Ologunagba da babban mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a, Kamaldeen Ajibade, SAN.

Jam'iyyar ta kafa kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban PDP na kasa (Kudu) Taofeek Arapaja da zai binciki laifuffukan da ake zargin jami'an biyu sun aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.