Filato: Jama'a Sun Fusata yayin da INEC ke Neman Jami'ai Ranar Zabe
- Masu kada kuri'a a jihar Filato ba su samu yadda su ke so ba bayan an samu wasu matsaloli a tsarin gudanar da zaben
- Rahotanni sun gano cewa an samu tsaiko saboda kin zuwan jami'an zaben INEC na wucin gadi wasu daga cikin mazauna
- Lamarin ya sa masu zabe daga wasu mazabun sun sauya wurin kada kuri'a zuwa kananan hukumomin da ke kusa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Masu kada kuri’a a jihar Filato sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda zaben kananan hukumomi ke gudana.
An samu rahoton rashin fara tantance masu zabe da wuri a wasu daga cikin mazabun da ke jihar.
A labarin da ya kebanta ga The Nation, an gano cewa an samu matsalar halartar jami'an zabe a wasu daga cikin kananan hukumomin Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba jami’an INEC a zaben Filato
Rahotanni sun bayyana cewa an samu rashin halartar jami’an zabe na wucin gadi daga hukumar INEC a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Lamarin ya jawo rashin jin dadin masu kada kuri’a a wasu mazabun da ke kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Gabas.
Filato: An samu lattin kayan zabe
Rahotanni sun tabbatar da cewa kayan zabe ba su isa wasu mazabu a jihar Filato da wuri ba duk da jama'a sun fito tun da sanyin safiya. A wasu wuraren, an samu jinkirin kayan gudanar da zaben har zuwa 11.00 na safe, yayin da masu zabe su ka hallara kusan 7.30 na safe.
An kuma gano hukumar INEC na kokarin maye gurbin jami'an da ba ta da su a lokacin gudanar da zaben.
APC ta yi zarra a zaben Binuwai
A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar APC ta doke dukkanin jam'iyyu wajen yin nasara a zaben kananan hukumomi 23 da ya gudana a jihar.
Shugaban hukumar zabe, Richard Tombowua ya bayyana nasarar da yan takarar APC su ka samu a zaben, sannan ya ce kansilolin jam'iyyar 276 sun yi nasara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng