Atiku ko Wike? Shugabanni Sun Bayyana Wanda Ya Haddasa Rikicin da Ya Mamaye PDP

Atiku ko Wike? Shugabanni Sun Bayyana Wanda Ya Haddasa Rikicin da Ya Mamaye PDP

  • Rikicin jam'iyyar PDP da ya ki ci ya ki cinyewa ya sake daukar sabon salo a ranar Talata a wani taronta da aka gudanar a birnin tarayya Abuja
  • Shugabannin PDP sun yi arangama a wajen taron inda aka samu rabuwar kai kan wadanda suka jawo rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar
  • Yayin da wasu ke ganin cewa Atiku Abubakar ya haddasa rikicin, wasu kuma sun ce Nyesom Wike ne musabbabin rabewar kawuna a PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun yi arangama a Abuja kan wadanda suka haddasa rikicin da ya dabaibaye ta.

Jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici tun bayan da aka gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

'Zancen bur inji tusa', APC ta fadi abin da zai faru a hadakar Kwankwaso da Peter Obi

Shugabannin PDP sun yi magana kan wanda ya haddasa rikicin jam'iyyar
An samu sabani a wani taron PDP kan wanda ya haddasa rikiicin jam'iyyar tsakanin Atiku da Wike. Hoto: @GovWike, @atiku
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya kuma taimaka wajen ba jam'iyyar APC mai mulki damar kayar da PDP a zaben da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wike ne silar rikicin PDP" - Ikenga

Wani dan majalisar wakilai, Hon Ikenga Ugochinyere, ya zargi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da haddasa rikicin da ke faruwa a jam’iyyar.

Hon. Ikenga Ugochinyere, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wani taro mai taken “Gyara PDP domin gyara Najeriya” a ranar Talata a Abuja.

Dan majalisar ya kuma zargi shugaban rikon PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum da tsohon gwamnan na Ribas, Nyesom Wike a matsayin matsalar jam’iyyar.

Ya ce:

"Me Damagum yake yi ne har yanzu? Ko za mu ci gaba da yin shiru mu ki fadin gaskiya? Muna gani Wike ya zama karen farautar APC, kowa ya san matsayinsa yanzu."

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

"Atiku ya jawo rikicewar PDP" - Ibrahim

Sai dai mataimakin sakataren yada labaran PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi ya soki bayanan Ugochinyere, inda ya dora laifin rikicin da ke faruwa a jam’iyyar kan Atiku Abubakar.

Yayin da yake dora alhakin matsalolin da ke faruwa a PDP kan Atiku, Abdullahi ya ce jam’iyyar Damagum ke jagoranta ba ta karkashin ikon Wike kamar yadda ake zargi.

"Atiku Abubakar ya yi nasarar kafa gwamnatin Buhari mafi muni a kan mu. Atiku ya bar jam’iyyar ne duk kokarin da wasu suka yi sannan ya sake dawowa kuma ya samu tikitin takara.
"Babu yadda za a yi a jajibirin zabe, gwamnoni biyar su yi wa wannan jam’iyya barazana kuma Atiku Abubakar ya nuna ko in kula tare da cewa su yi duk abin da za su iya."

Damagun ya taimakawa Wike a PDP?

A wani labarin, mun ruwaito cewa mukaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya ce ko kadan bai ba Nysome Wike goyon baya a taron jam'iyyar na kasa ba.

Kara karanta wannan

Fubara ya lallasa Wike: Bakuwar jam'iyya ta lashe kujerun ciyamomi 22 a Ribas

A cewar Damagum, ya na da alaka mai karfi da Atiku Abubakar da shi kansa Wike, kuma ministan Abujan ya bayyana bai samu wani taimako daga gare shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.