Sanata Barau Ya Rikita NNPP a Kano, Daruruwan 'Yan Kwankwasiyya Sun Sauya Sheka

Sanata Barau Ya Rikita NNPP a Kano, Daruruwan 'Yan Kwankwasiyya Sun Sauya Sheka

  • Daruruwan 'yan jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) mai mulki a jihar Kano ne suka sauya sheka zuwa APC a ranar Talata
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya ce ya karbi daruruwan 'yan Kwankwasiyyar da suka sauya sheka a Abuja
  • A cikin 'yan kwanakin nan ana ci gaba da samun masu sauya sheka daga NNPP zuwa APC musamman ta hannun Sanata Barau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya sake gigita NNPP mai mulki a jihar Kano yayin da ya karbi daruruwan 'yan Kwankwasiyya.

A makon da ya gabata Sanata Barau Jibrin ya karbi daruruwan ‘yan jam’iyyar NNPP a fadin kananan hukumomin 44 na jihar Kano zuwa APC.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan 'yan Kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa APC
Daruruwan 'yan NNPP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kano. Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

Kano: Daruruwan 'yan NNPP sun koma APC

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a daren ranar Talaya, Sanata Barau ya ce daruruwan ‘yan NNPP daga Kano sun sake sauya sheka zuwa jam’iyyarsu ta APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"A makon da ya gabata mun karbi daruruwan ‘yan jam’iyyar NNPP daga fadin kananan hukumomin jihar mu 44.
"Amma a yau daruruwan ‘yan NNPP ne daga karamar hukumar Shanono ta Kano suka shigo jam’iyyar APC."

Su wanene suka koma APC a Kano?

Sanata Barau ya ce wadanda suka sauya shekar sun same shi a ofishinsa da ke a majalisar tarayya karkashin kungiyoyi biyar.

"Kungiyoyin su ne; Kungiyar mafarautan Kwankwasiyya, karkashin jagorancin Murtala Abubakar Kwamanda da kungiyar matasan Kwankwasiyya karkashin Murtala Sani.
"Sauran su ne; Kwankwasiyya Miyetti Allah, karkashin Ja'e Adamu; masu kare Kwankwasiyya a rediyo, karkashin Abdullahi DPO da mahautan Kwankwasiyya, karkashin Sulaiman Bala Mainama."

Kara karanta wannan

Doguwa: 'Dalilin da ya sa 'yan Kwankwasiyya ke sauya sheka zuwa APC a Kano'

Alin Kano ya ziyarci Barau a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa daya daga cikin kusoshin siyasa daga jam'iyyar PDP a jihar Kano ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Alhaji Abdullahi Ali, watau Alin Kano ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa APC bayan shafe shekaru 30 yana koyi da kayawawan ɗabi'un Sanata Barau Jibrin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.