Rikicin Rivers: Wike Ya Bayyana Abin da Zai Kawo Zaman Lafiya
- Nyesom Wike ya samo mafita kan rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
- Ministan babban birnin tarayya Abuja ya buƙaci Gwamna Siminalayi Fubara na jihar ya bi umarnin kotu domin a samu zaman lafiya
- Wike ya bayyana cewa bin doka da oda shi ne abin da zai tabbatar an samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin kowa a jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, shawara kan rikicin da yake faruwa a jihar.
Nyesom Wike ya buƙaci magajin nasa da ya riƙa bin doka da oda domin a samun zaman lafiya a jihar.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels tv a shirinsu na 'Politics Today'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Wike ya ba da?
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa bin doka da oda shi ne abin da yake kawo zaman lafiya.
"Ana samun zaman lafiya idan aka bi doka da oda. Ana samun zaman lafiya idan aka bi hukuncin da kotu ta yanke."
"Ka bi umarnin kotu sannan ka bari doka ta yi aikinta. Idan ka ƙi bin doka da oda, kana gayyato rashin zaman lafiya ne."
- Nyesom Wike
An samu rikicin siyasa a Rivers
Kalaman na Wike na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar Rivers mai arziƙin man fetur.
Jihar da ke a yankin Kudu maso Kudu ta samu kanta ciki rikicin siyasa sakamakon taƙaddamar da ake yi tsakanin Wike da Gwamna Fubara.
Tinubu ya magantu kan rikicin Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan rikicin bayan zabe ya fara ƙamari a jihar Rivers.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamna Siminalayi Fubara da dukkan yan siyasa a Rivers su mayar da wuƙaƙensu.
Shugaba Tinubu ya ce ya zama dole a girmama doka da oda tare da yin taka-tsantsan kan rikicin da yake faruwa jihar mai arziƙin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng