Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin Barkewar Rikici a Jihar Rivers

Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin Barkewar Rikici a Jihar Rivers

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya taɓo batun rikicin da ke aukuwa a jihar Rivers mai arziƙin man fetur
  • Wike ya bayyana cewa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ne ke da alhaki kan abubuwan da suke faruwa a jihar a yanzu
  • Ministan ya zargi gwamnan da rashin bin umarnin kotu wanda a cewarsa hakan miƙa katin gayyata ne ga rashin zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicin jihar Rivers.

Nyesom Wike ya zargi magajinsa watau gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da ƙin bin umarnin kotu.

Wike ya magantu kan rikicin Rivers
Wike ya zargi Gwamna Fubara da rashin bin umarnin kotu Hoto: @Jmartinsijere, @possible1001
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya bayyana abin da zai kawo zaman lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya zargi Gwamna Fubara

A cewar Nyesom Wike idan har ana ƙin bin hukuncin da kotu ta yanke, tabbas ana gayyato rashin zaman lafiya a jihar.

"Na yi gwamna, a kodayaushe ina bin doka. Kun ji gwamnan yana cewa jihar mu ta koma kama karya inda mutane ke ƙin bin doka da oda."
"Dole ne a ka bi hukuncin kotu. Ka da ka ɗauki doka a hannunka. Da zarar ka ƙi yin biyayya ga hukuncin kotu, ka na gayyatar rashin zaman lafiya, ka na gayyatar tashin hankali."

- Nyesom Wike

A cewar Wike, Gwamna Fubara ne ke da alhaki kan rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke jihar mai arzikin mai a ranar Lahadi.

Karanta wasu labaran kan rikicin Rivers

Kara karanta wannan

"Durkusawa wada:" Gwamnan Ribas ya fadi dalilin ba Wike hakuri

Gwamna Fubara ya ba Wike haƙuri

A wani labarin kuma, kun ji gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya roki Ministan Abuja kuma tsohon uban gidansa, Nyesom Wike kan samuwar zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa sai da ya durkusa har kasa domin lallaba Nyesom Wike, wanda tsohon gwamnan Rivers ne domin dakatar da tashin hankali a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng