Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Hanyar Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya bayyana cewa zai yi wahala a iya kayar da shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
- Salihu Lukman ya ce tsare-tsaren da jam'iyyun adawa suke da shi ba zai ba 'yan kasar kwarin guiwar zabarsu a babban zaben mai zuwa ba
- Tsohon kusa a APC ya ce akwai bukatar a samar da jam'iyyar adawa da al'umma da kasar ce kawai a gabanta ba wai fitar da 'yan takara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsohon mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya bayyana abin da ka iya faruwa da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Salihu Lukman ya ce jam'iyyar adawa da ke da alaka mai karfi da 'yan Najeriya ce kadai za ta iya kayar da Shugaba Bola Tinubu idan ya nemi tazarce a 2027.
Yadda za a kayar da Tinubu - Lukman
A wata sanarwa da jaridar Leadership ta samu a jiya, Lukman ya ce samun jam'iyyar da za ta iya kayar da Tinubu abu ne mai matukar wahala saboda 'yan Najeriya sun sare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a yanzu 'yan Najeriya ba za su kara yarda da duk wani dan siyasa da zai yi masu alkawarin iska ba bayan da jam'iyyar APC ta gaza cika alkawuran da ta dauka a 2015.
Salihu Lukman ya nuna cewa batun a nemi tsige APC ko shugaba Tinubu a 2027 ta hanyar 'yan dabaru ba zai cimma gaci ba, dole ana bukatar babban shiri na kai kasar 'tudun mun tsira.'
Lukman ya magantu kan jam'iyyun adawa
Tsohon jigon na APC ya ce abu na farko shi ne a san wacce iriyar jam'iyyar adawa ake son kafawa, wacce za ta rika samar da 'yan takara domin zabe kawai?
Lukman ya ce idan aka ce manufar jam'iyyar kenan, to kasar za ta sake samun sabuwar jam'iyya marar karfi da ba ta da bambanci da APC, PDP, LP, NNPP da sauransu.
Ya nemi 'yan siyasar adawa da su kauracewa ire-iren jam'iyyun da ba su da wata manufa sai ta fitar da 'yan takara wadanda ke haddasa rikicin dimokuradiyya a kasar inji rahoton The Sun.
Salihu Lukman ya caccaki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban APC na kasa, Salihu Lukman ya caccaki Bola Tinubu saboda ba ya bari ana ganinsa.
Lukman ya bayyana cewa marigayi Sani Abacha ya fi ba mutane damar haduwa da shi fiye da yadda a yanzu Tinubu ya ke yi, inda ganinsa sai wane da wane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng