Buba Galadima Ya Fayyace Jawabin Kwankwaso kan Hadaka da Peter Obi

Buba Galadima Ya Fayyace Jawabin Kwankwaso kan Hadaka da Peter Obi

  • Daya daga cikin jagororin NNPP, Buba Galadima ya ce mutane ba su fahimci bayanan da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba
  • Buba Galadima ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso mai biyayya ne ga shugabannin da su ka cancanci a yi masu biyayya
  • Ya kara bayani a kan maganar da Kwankwaso ya yi na yiwuwar zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Peter Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Guda daga cikin jiga-jigan jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa jama’a ba su fahimci bayanin da Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi ba.

Buba Galadima wanda guda ne daga cikin makusantan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce wadanda ba sa fahimtar harshen Hausa ne su ka juya batun.

Kara karanta wannan

'Zancen bur inji tusa', APC ta fadi abin da zai faru a hadakar Kwankwaso da Peter Obi

Tinubu
Buba Galadima ya yi bayanin furucin Kwankwaso kan zaben 2027 Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

A tattaunawar BBC Hausa da Buba Galadima, ya ce jama’a na ta yada cewa Sanata Kwankwaso zai karbi tayin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Peter Obi na jam’iyyar LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tafiyar Kwankwaso ta talakawa ce:" Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima ya kara da cewa tafiyar kwankwasiyya ta taimakon talakawa ce, saboda haka babu zancen karbar tayin mataimakin shugaban kasa.

Kan kalamanm jam’iyyar LP na yin maraba da Sanata Kwankwaso a matsayin mataimakin Peter Obi, Buba Galadima ya ce su na batun ne domin nuna cewa kofarsu a bude ta ke.

“Kwankwaso na bin wanda ya cancanta:” Buba Galadima

Jagora a NNPP, Sanata Buba Galadima ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso mai biyayya ne.

“Ai ya bi, wa ya bi? Bai bi Buhari ba? Bai bi Atiku ba?

- Buba Galadima

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi illar gobarar kasuwa ga Kano, Abba ya yi wa 'yan kasuwa alkawari

APC ta magantu kan hadin Kwankwaso da Obi

A baya mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta ce Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi ba za su iya hada kansu don tunkarar zabe ba.

Ra’ayin APC na zuwa ne bayan an samu rade-radin cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce zai iya hadewa da Peter Obi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.