'Zancen Bur Inji Tusa', APC Ta Fadi Abin da Zai Faru a Hadakar Kwankwaso da Peter Obi
- Yayin da ake shirin haɗaka tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, jam'iyyar APC ta yi tsokaci kan lamarin
- Jam'iyyar ta ce babu wani abin tsoro a gare ta saboda dukansu yan son rai ne babu mai amincewa da haka
- Hakan ya biyo bayan jita-jitar cewa Kwankwaso ya amince da tayin zama mataimakin Peter Obi amma kan wasu sharuda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta yi martani game da shirin haɗaka tsakanin jam'iyyar NNPP da kuma LP.
APC ta ce ko a jikinta ba ta damu da shirin haɗaka tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi na jam'iyyar LP ba.
APC ta soki haɗakar Kwankwaso da Obi
Daraktan yada labaran jam'iyyar ta kasa, Bala Ibrahim shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim ya ce wannan shiri babu inda zai je saboda an gwada yin haka a zaben 2023 da ya gabata.
Ya ce son rai da rashin yadda shi zai fara hada su fada saboda babu wanda zai sadaukar da neman takararsa ga wani.
Haɗakar NNPP-LP: APC ta fadi abin da zai faru
"Babban abin da zai wargaza wannan tafiya bai wuce rashin yadda a tsakaninsu ba wanda shi ne zai kawo cikas."
"Babu yadda za su yi nasara har sai idan akwai yadda a tsakaninsu wanda an gwada a baya ba a yi nasara ba."
"Da Kwankwaso da Obi sun sake shirin haɗaka wanda suka yi a baya da bai yi tasiri ba, dukansu suna da burin zama shugaban kasa babu mai sadaukar da haka ga dan uwansa."
- Bala Ibrahim
Ibrahim ya ce ko kadan hakan ba zai damu jam'iyyar APC ba saboda ta sani za a maimaita abin da ya faru ne a baya.
Haɗakar Kwankwaso, Obi ta fara karfi
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana kan yiwuwar yin haɗaka da dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi.
Haka zalika jam'iyar LP ta yi martani da ke nuna amincewa da hadakar bayan maganar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng