'Mene Dalilin Kiran Sunana Kadai', Gwamna Ya Kalubalanci Tinubu kan Rigimar Ribas
- Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna damuwa kan matsayar da Bola Tinubu ya dauka game da rikicin Rivers
- Sumi Fubara ya ce bai ji dadin yadda Tinubu ya kira sunansa shi kadai ba bayan kowa ya san inda matsalar take
- Hakan ya biyo bayan samun rigimar da ya yi sanadin rasa rayuka da kona dukiyoyi bayan zaben kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamna Siminalayi Fubara ya yi magana kan rikicinsa da tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
Mai girma Simi Fubara ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya kira sunansa shi kadai yayin maganarsa a kan rikicin.
Bola Tinubu ya magantu kan rigimar jihar Rivers
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin faifan bidiyon YouTube da Channels TV ta wallafa a daren jiya Litinin 7 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan martanin Tinubu kan rigimar da ta ki karewa inda ya ba Gwamna Fubara shawara.
Tinubu ya bukaci Fubara da sauran yan siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar su nuna juriya da kuma bin doka da oda.
Gwamna Fubara bai ji dadin kalaman Tinubu ba
Fubara ya ce ba shi da matsala da tsoma baki da Tinubu ya yi amma ya ce kowa ya san inda matsalar take.
Ya ce ba shi ne babbar matsala ba a rikici tsakaninsa da tsohon mai gidansa, Nyesom Wike.
"Ba ni da wata matsala da tsoma baki da Tinubu ya yi, damuwa ta shi ne yadda ya kira sunana ni kadai."
"Wannan abu ne mai sauki, kowa a jihar Rivers ya san daga inda matsalar take, ba Fubara ne matsala ba."
- Siminalayi Fubara
Fubara ya fadi musabbabin kara rikicewar matsalar a jihar bayan kammala zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar.
Gwamna Fubara ya shawarci Wike kan rigimar Rivers
Kun ji cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya roki Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya bar rigimar jihar ta wuce.
Gwamnan ya ce bai kamata tsohon gwamnan ya ce sai ya yi nasara kan dukan fadan da ya ke yi ba musamman a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng