Jigawa da Ribas: Yadda Aka Ci Yan Adawa da Yaki a Zaben Kananan Hukumomi

Jigawa da Ribas: Yadda Aka Ci Yan Adawa da Yaki a Zaben Kananan Hukumomi

Jihohi hudu ne - Jigawa , Ribas, Binuwai da Akwa Ibom ne su ka gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar Asabar 5 Oktoba, 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Daga cikin zabukan kananan hukumomin, biyu sun yi matukar daukar hankali saboda dalilai mabanbanta.

Zaben
Zabukan kananan hukumomin Jigawa da Ribas sun zo da sabon salo Hoto: Abdullahi Bego/Niger Delta Insider
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tattaro abubuwan da su ka dauki hankali a zaben kananan hukumomin Jigawa da Ribas.

1. Yan adawa sun kaurace wa zaben Jigawa

A ranar 5 Oktoba, 2024 ne aka gudanar da zabe cikin ruwan sanyi a kananan hukumomin jihar Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

Amma yan adawa ba su ji dadin yadda zaben ya gudana ba, sai dai ana ganin ba a yi hatsaniya ba ne saboda wanzuwar zaman lafiya a jihar.

"Yan takarar Ciyamomi hudu ne ba na APC ba." "Akwai Ciyamomin da su ka tsaya daga NNPP, akwai wanda su ka tsaya kuma a jam'iyyar PDP."

- Habib Yusuf, kakakin hukumar zabe ta jihar Jigawa

Labarin da ya tabbata shi ne babu wani dan jam'iyyar adawa da ya samu nasara a zama Ciyaman, amma an samu Kansiloli daga APGA da Accord.

Sai dai a tattaunawar Legit da shugaban PDP na Jigawa, Ali Idris Diginsa, ya ce an yi zaben Jigawa ne kawai, amma kamar ba a yi ba.

A martanin APC ta bakin sakataren jam’iyyar reshen Jigawa, Muhammad Dikuma Umar ya ce jam'iyyun adawa sun firgita ne saboda irin ayyukan da gwamnatin APC ke yi a jihar amma ba don rashin adalci ba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

2. Ribas: An yi zabe cikin tashin hankali

Zaben Ribas ya kafa tarihi ganin yadda gwamnatin jihar ta yi biris da umarnin kotu, aka kuma yi zabe mai cike da sarkakiya da tashin hankali.

Lamarin ya biyo bayan rikici da ke tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da dan tsohon maigidansa kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Jaridar The Premium Times ta wallafa yadda aka rika samun kone-kone hedkwatar kananan hukumomi bayan kammala zaben.

Masani ya fadi kuskure a zaben kananan hukumomi

Adnan Mukhtar Tudun Wada, tsohon dan takarar majalisar jiha ne a Kano, ya ce jam'iyyun hamayya na fargabar hukumomin zabe a jihohi ba za su yi masu adalci ba.

Ya yi zargin cewa wasu lokutan a kan yi kama-karya, wanda ke sa yan jam'iyyun adawa ba sa samun kujeru a kananan hukumomi sosai.

Gwamna ya rantsar da shugabannin kananan hukumomi

A baya kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya rantsar da shugabannin kananan hukumomi da su ka yi nasara a zaben da ya gudana ranar Asabar.

Gwamna Umar Namadi ya gargade su da su tabbatar da gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci sakaci da hakkokin jama'a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.