Abubuwa 3 da Suka Jawo Karamar Jami’yya Ta Buga APC da PDP a Kasa a Rivers
- A ranar Asabar da ta wuce aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Rivers karkashin gwamna Siminalayi Fubara
- Zaben ya zo da sabon salo yayin da karamar jami'yya ta APP ta buga manyan jam'iyyu kamar su APC da PDP mai mulki a jihar Rivers
- A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin abubuwa da ake ganin su suka jawo jami'yyar APP kafa tarihin samun nasara a Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Gwamnatin Siminalayi Fubara ta gudanar da zaben kananan hukumomi a Rivers a ranar Asabar.
Zaben ya bar baya da kura inda aka samu rikici da ƙone ƙone kuma manyan jam'iyyun Najeriya sun sha ƙasa.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu abubuwa da ake ganin su suka jawo nasara ga APP a kan irinsu PDP da APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da suka jawowa APP nasara a Rivers
1. Jajircewan masu zabe
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana ra'ayin cewa masu zabe a Rivers sun nuna jajircewa wajen zaben wanda suke so.
Atiku Abubakar ya wallafa a Facebook cewa hakan ya nuna masu zabe sun nuna rashin tsoro kuma hakan ya dace a yi a tsarin dimokuraɗiyya.
2. Rikicin manyan jam'iyyu
Manyan jam'iyyun, PDP da APC sun samu sabani da gwamna Siminalayi Fubara wanda har suka tafi zuwa kotu.
Bayan shiga kotu, an dakatar da yin zaben amma gwamna Fubara ya ce babu fashi wanda hakan ya saka jam'iyyun ba su samu karfin gwiwa ba a lokacin zaben.
3. Rikicin Fubara da Wike
Gwamna Simi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike suna takun saƙa a PDP, wannan ya sa mutanen Fubara su ka koma APP.
Ana ganin hakan na cikin manyan abubuwan da suka sanya gwamna Fubara rungumar APP da kuma juya baya ga PDP a zaɓen.
4. Hukuncin kotun tarayya
An rahoto cewa kotu ta kawo cikas ga zaben wanda hakan ya jawo jami'an tsaro su ka taka rawar gani wajen gudanar da shi.
The Cable ta rahoto yadda manyan jam'iyyu suka kauracewa zaben da aka shirya duk da alkali sun yi hukuncin da ya kawo tasgaro.
Rikici ya biyo bayan kammala zaben Rivers wanda aka samu kone koke a ƙananan hukumomin jihar.
Tinubu ya yi magana kan zaben Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gargadi bayan rikici ya biyo bayan zaben kananan hukumomi a jihar Rivers.
Bola Ahmed Tinubu ya ba sufeton yan sandan Najeriya umarnin shawo kan rikicin tare da tabbatar da doka da oda a dukkan sassan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng