Gwamna Ya Rantsar da Zababbun Ciyamomin APC, Ya Ja Musu Kunne
- Gwamnan Jigawa ya rantsar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 27 da aka zaɓa a jihar
- Umar Namadi ya ja kunnen ciyamomin a kan aikata ayyukan da suka saɓawa doka yayin gudanar da mulkinsu
- Ya umarce su da su koma zama a hedkwatar ƙananan hukumomin domin al'ummar su na buƙatar su kasance can
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Mai girma Gwamna Umar Namadi ya kuma gargaɗe su da su guji raba filaye ba bisa ƙa'ida ko su fuskanci ɗauri.
Jaridar Tribune ta ce a ranar Asabar da ta gabata ne aka zaɓi shugabannin ƙananan hukumomin guda 27 waɗanda dukkaninsu ƴan jam’iyyar APC ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Umar Namadi ya umarci ciyamomin da su maida iyalansu zuwa hedkwatar ƙananan hukumominsu domin su ci gaba da rayuwa a can.
Wane gargaɗi Gwamna Namadi ya yi?
"Ina gargaɗin ku da ku guji rabon gonaki da sayar da filayen kiwo da gandun daji a yankunan ku ba bisa ƙa'ida ba."
"Yanzu ba lokacin zama ba ne a Kano, Abuja ko Dutse alhali kana shugaban ƙaramar hukumar Buji, Guri ko Kafin Hausa."
"Dole ne ku zauna a yankinku a koda yaushe domin ana buƙatar ku a kowane lokaci."
"Akwai gidaje masu kyau na ciyamomi a a dukkanin ƙananan hukumomin 27. Ku gyaru su idan suna cikin yanayi mara kyau."
"Amma dole ne ku zauna tare da mutanenku domin ku sauke nauyin da ke wuyanku yadda ya dace."
- Gwamna Umar Namadi
Gwamna Alia ya rantsar da ciyamomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Gwamna Alia ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomin ne a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoban 2024 a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Makurdi.
Alia ya buƙace su da su yi aiki tare da ƴan adawa ta hanyar karɓar shawarwari da gyare-gyare masu ma'ana domin samar da shugabanci nagari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng