Zaben 2027: Jigon APC Ya Bayar da Shawara kan Takarar Bola Tinubu

Zaben 2027: Jigon APC Ya Bayar da Shawara kan Takarar Bola Tinubu

  • Wani babba a APC, Abayomi Mumuni ya ga rashin dacewar magana kan sake tsayar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu takara a 2027
  • Ambasada Abayomi Mumuni na wannan batu ne a lokacin da wasu daga cikin yan APC ke cewa za su marawa sake tsayar da Tinubu takara
  • Jigon ya bayyana illar abin da wasu yan jam'iyyar su ke yi, tare da bayar da shawara kan abin da ya fi kamata a mayar da hankali a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Dattijo a APC, Ambasada Abayomi Mumuni ya ba sauran yan jam'iyyar shawara kan batun takarar Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

An samu wasu manya a jam'iyyar da ke kokarin neman hada kawunan sauran yan APC don sake tsayar da Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Tinubu
2027: Jigon APC ya nemi a dakata da batun takarar Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa a ra'ayinsa, Ambasada Abayomi Mumuni na ganin ya yi wuri a fara zancen sake fitar da dan takara lokacin da ake tsaka da gudanar da gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Illar magana kan takarar Tinubu a 2027

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa jigo a APC reshen jihar Legas, Abayomi Mumuni ya ce maganar sake tsayar da Tinubu takara zai dauke hankalinsa daga abin da ya dace.

Mumuni ya kara da cewa yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali kan ayyukan raya kasa ba takara ba.

Tinubu 2027: Jigon APC ya ba da shawara

Kara karanta wannan

ACF: Kungiyar dattawa ta fadi yadda rashin tsaro ke neman shafe Arewa

Ambasadan ya shawarci sauran yan jam'iyyar APC su jingine batun takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

"A wannan lokaci da kasarmu ke fama da matsalolin da tsofaffin gwamnatoci su ka haddasa, kamata ya yi a mayar da hankali kan magance matsalolin da su ka addabi Najeriya."

- Ambasada Abayomi Mumuni

An fallasa shirin wasu 'yan APC kan Tinubu

A baya mun wallafa cewa daya daga cikin yan jam'iyya mai mulki ta APC, Garus Gololo ya bayyana shirin da su ke yi kan sake tsayar da Bola Tinubu takarar shugaban kasa.

Dakta Gololo ya bayyana cewa babu yadda za a yi su amince a sake tsayar da shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar su a kakar zaben 2027 mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.