‘Ba Za Mu ba Tinubu Takara ba,’ Jigon APC Ya Tono Wani Shiri kan Zaben 2027
- Kusa a jami'yyar APC kuma mai fashin baki, Garus Gololo ya ce za su tabbatar da cewa Bola Tinubu bai samu takara ba a 2027
- Dakta Garus Gololo ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da gwamnatin tarayya ta ke yi wanda suka jefa al'umma a wahala
- Gololo ya kuma yi wasu bayanai kan ambaliyar ruwan da ta faru a Maiduguri da lalacewar wasu hanyoyin Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai fashin baki kuma jigo a APC, Garus Gololo ya yi bayani kan halin wahalar rayuwa da ake ciki a Najeriya.
Dakta Garus Gololo ya ce za su tabbatar Bola Ahmed Tinubu bai samu tikitin tsayawa takara a zaben 2027 mai zuwa ba.
Legit ta tatttaro bayanan da Garus Gololo ya yi ne a cikin wani bidiyo da Abdullahi A. Abdullahi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar hana Tinubu takara a 2027
Dakta Garus Gololo ya ce a matsayinsa na jigon APC ba za su bari shugaba Bola Tinubu ya samu takara a zaɓen 2027 ba.
Jigon jam'iyyar ya ce tun a zaben fitar da gwani za su kayar da Bola Ahmed Tinubu domin sun san yan Najeriya ba za su zabe shi ba.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kawo yunwa a Najeriya saboda haka ba za su iya kira a zabi wanda ya kawo yunwa ba.
Garus Gololo yana nan a APC daram
Garus Gololo ya ce ba wanda ya isa ya kore shi a APC saboda su suka yi wa jam'iyyar hidima tun daga shekarar 2015 zuwa yau.
Saboda haka ya ce ya kashe kudi kimanin Naira biliyan 15 a APC kuma idan za a kore shi dole sai an biya shi kudin da ya kashewa jami'yyar.
Gololo ya kuma koka kan cewa kudin da aka ba Borno saboda ambaliya ya yi kadan sannan ya ce hanyoyin Arewa duk sun lalace.
2027: LP da NNPP sun fara zancen hadaka
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana kan yiwuwar yin haɗaka da Peter Obi na LP.
Haka zalika jam'iyar LP ta yi martani da ke nuna amincewa da hadakar bayan maganar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng