Doke Tinubu a 2027: Hadakar Kwankwaso da Peter Obi Ta Fara Samun Ƙarfi

Doke Tinubu a 2027: Hadakar Kwankwaso da Peter Obi Ta Fara Samun Ƙarfi

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana kan yiwuwar yin haɗaka da dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi
  • Haka zalika jam'iyar LP ta yi martani da ke nuna amincewa da hadakar bayan maganar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi
  • Tun kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2023 jam'iyyun LP da kuma NNPP suka fara maganar haɗaka amma abin bai yiwu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Maganar haɗaka tsakanin Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi a kan zaben shekarar 2027 ta fara yin karfi.

Bayan bayanin Kwankwaso kan yiwuwar haɗakar, jam'iyyar LP ta yi maratanin cewa ta yi na'am da abin da ya fada.

Kara karanta wannan

Wasu miyagu sun buɗe wuta a kusa da gidan Ministan Tinubu, sahihan bayanai sun fito

Obi Kwnakwaso
LP ta yi magana kan hadaka da NNPP. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso|Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa sakataren jam'iyyar LP, Umar Faruk ne ya tabbatar mata da amincewa da batun yin hadakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar haɗakar Peter Obi da Kwankwaso

A wata hira da Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi, ya nuna zai amince da yin haɗaka da Peter Obi a zaben mai zuwa na 2027.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce duk da ya fi Obi karfi a siyasa zai iya zama mataimakinsa idan aka cika wasu sharuda.

Martanin LP kan haɗakar Obi da Kwankwaso

Sakataren LP na kasa, Umar Faruk ya nuna amincewa da yin haɗaka tsakanin Kwankwaso da Peter Obi.

Umar Faruk ya ce jam'iyyar LP ta yi na'am da yardar Rabi'u Kwankwaso ya kasance mataimakin Peter Obi a zabe mai zuwa.

Jam'iyyar LP ta ba Rabiu Kwankwaso shawara

Jam'iyyar LP ta ce ya kamata Kwankwaso ya cigaba da ƙoƙarin tattalin maganar hadakar kada ya rudu da cewa yana da farin jini a Arewa.

Kara karanta wannan

'Za mu fitar da taruraro a kowane gida,' Kwankwaso ya yi albishir ga talakawa

Sakataren na LP ya kara da cewa Peter Obi ya samu kuri'u sama da miliyan 6 alhali Kwankwaso bai samu ko miliyan 2 ba wanda hakan zai sa Kwankwaso ya bi bayan Obi.

Jigon APC ya yi watsi da hadakar yan adawa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan hadakar jiga-jigan jam'iyyun adawa game da zaben 2027.

Iliyasu Kwankwaso ya ce Atiku Abubakar da Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi suna bata lokacinsu ne kan shirin kifar da Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng