Gwamnan Bauchi Ya Yabi Fubara kan Bijirewa 'Kutse' a Zaben Kananan Hukumomin Ribas
- Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed ya yaba da yadda aka gudanar da zabe a jihar Ribas
- A ranar Asabar ne gwamnatin Siminalayi Fubara ta bijirewa umarnin kotu da barazanar jami'an tsaro, aka yi zabe
- Ciyamomi da Kansiloli daga jam'iyyun adawa na APP ne su ka yi nasarar samun kujerun da ke kananan hukumomi 22
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya yabi yadda gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya yi tsayin daka wajen zaben kananan hukumomi.
Dambarwar da ke tsakanin tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike da gwamna mai ci a jihar ta kutsa cikin siyasa har ta so ta shafi zaben kananan hukumomi.
A bidiyon da Abban Atiku ya wallafa a shafinsa na X, gwamna Bala Mohammed ya ce Siminalayi Fubara ya nuna karfin ikon gwamnatin jiha a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ka zama jigo a siyasa:" Gwamnan Bauchi ga Fubara
Channels Television ta wallafa cewa gwamna Bala Mohammed ya bayyana dagewar Siminalayi Fubara na gudanar da zaben kananan hukumomi a Ribas da bude wani sabon shafi a siyasar kasa.
Ya bayyana cewa abin da gwamnan ya yi ya kara fito da martabar gwamnoni a kasar nan, tare da nuna kishin Fubara na tabbatar ga dimokuradiyya duk da PDP ba ta yi nasara ba.
"Fubara dan PDP ne" Inji Gwamnan Bauchi
Shugaban kungiyar gwamnonin na PDP, Bala Mohammed ya jaddada cewa gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara cikakken dan PDP ne, kuma shi ne ma mataimakinsa.
Ya na wannan batu ne yayin da ake rade-radin gwamna Fubara zai iya watsar da PDP yayin da rikicin da ke tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi kamari.
Gwamna Fubara zai rantsar da Ciyamomi
A baya kun ji cewa gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya shirya rantsar da yan takara da su ka yi nasara a zaben kananan hukumomin jihar da ya gudana a ranar Asabar.
A ranar 6 Oktoba, 2024 ne gwamnan ya rantsar da Ciyamomi 23 da Kansilolin da su ka yi nasara a zaben kananan hukumomin da yan jam'iyyar adawa ne su ka yi nasara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng