Sauye Sauye a Majalisar Ministoci: Tinubu Zai Saki Sunayen Ministocin da Zai Kora

Sauye Sauye a Majalisar Ministoci: Tinubu Zai Saki Sunayen Ministocin da Zai Kora

  • Shugaba Bola Tinubu ya kammala shirin yiwa majalisar ministocinsa garambawul inda ake sa ran nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwar
  • A cikin matsin lamba da ake samu sakamakon kalubalen tattalin arziki da zanga-zanga, Tinubu na da burin sallamar ministocin da ba sa yin aiki
  • Garambawul din zai kunshi manyan sauye-sauye, gami da yuwuwar rushewa da hadewar wasu ma'aikatun gwamnatintarayyar kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A wani gagarumin ci gaba, rahotanni sun ce Shugaba Bola Tinubu ya kammala rubuta sunayen ministocin da zai kora yayin da zai yi garambawul a majalisar ministoci.

Majiyoyi da dama daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa shugaban kasar ya kammala rubuta sunayen ministocin da za a sallama da kuma wadanda za a ci gaba da aiki da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gama tsara sunayen ministocin da zai kora daga aiki, bayanai sun fito

Majiya daga fadar shugaban kasa ta ce an kammala shirin yiwa majalisar ministoci garambawul
Za a bayyana sauya 'yan majalisar ministocin Tinubu da za a sallama. Hoto: @officalABAT
Asali: Twitter

Lokacin sakin sunayen ministoci

A daren ranar Alhamis ne ake sa ran fitar da jerin sunayen, jim kadan bayan Tinubu ya isa kasar Birtaniya domin hutun makonni biyu na shekara inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wani taron kwana uku da 'yan majalisar ministoci da masu taimakawa shugaban kasa suka yi a watan Nuwamban da ya gabata, Tinubu ya sanar da kafa sashen CDCU.

Wannan sashen wanda ke karkashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Hadiza Bala-Usman, zai auna ayyukan ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.

Tinubu ya jadadda cewa wadannan rahotannin ayyukan da ake sashen zai tattara na lokaci-lokaci za su tantance wadanda za su ci gaba da aiki da shi da kuma wadanda za a sallama.

An kammala shirin garambawul

Jami'an gwamnati da suka yi magana a Juma’a tare da nemana sakaya sunayensu, sun bayyana cewa an kammala shirin garambawul din, wanda Tinubu ke nazari a kai.

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

"Muna jiran izini ne kawai mu aiwatar da sauye sauyen. Yanzu muna jiran Tinubu ya aiko mana da sunayen wadanda yake son ya sauke da wadanda yake so ya nada.
"Bayan gabatar masa da rahoton, ya ce zai yi nazari a kai kafin ya ba da izinin fitar da sunayen. Ina tunanin ya na son sauye wasu sunayen ne, amma dai muna jiransa."

- A cewar wata majiya.

A halin yanzu dai al'ummar Najeriya sun mayar da hankali kan wannan garambawul da Tinubu zai yi domin ganin wadanda zai kora da kuma wadanda za a nada.

Tinubu zai kori Femi Gbajabiamila?

A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu zai kori shugaban ma'aikan fadarsa, Femi Gbajabiamila, a yayin yiwa majalisar ministocinsa garambawul.

Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa Tinubu ya rubuta sunan tsohon minista, Babatunde Fashola, a matsayin wanda zai gaji Gbajabiamila idan aka tashi yin garambawul din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.