Neman Tazarce a 2027: Manyan 'Yan Siyasar Kano da Ke Goyon bayan Shugaba Tinubu

Neman Tazarce a 2027: Manyan 'Yan Siyasar Kano da Ke Goyon bayan Shugaba Tinubu

Kano – Ana kallon jihar Kano a matsayin wata babbar cibiyar siyasa a kasar Najeriya, kuma galibi tana taka rawa a zaben shugaban kasa wajen tara yawan kuri'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai samu nasara a Kano a zaben 2023 ba, amma a halin yanzu shugaban na Najeriya ya na da goyon bayan wasu manyan ‘yan siyasa a jihar.

Wasu jiga jigan 'yan siyasar Kano da ke goyon bayan Tinubu
Zaben 2027: Tinubu na da goyon bayan Ganduje da wasu jiga jigan 'yan siyasar Kano 2. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Goyon bayan wadannan jiga jigan 'yan siyasa a jihar da ke Arewa maso Yamma zai iya taimakawa Tinubu ya samu tazarce idan ya fito takara a zaben 2027.

Baya ga Olusegun Obasanjo, babu wani shugaban kasa daga kudanci da ya taba mulkin Najeriya shekaru 8 a jere tun bayan da kasar ta koma kan mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999.

Kara karanta wannan

"Ba na maganar 2027": Tinubu ya magantu kan zabe, ya fadi abin da ke gabansa a yanzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan siyasar Kano magoya bayan Tinubu

Sai dai alkaluma na nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu na iya karya wannan kadarin idan har ya fito zabe a 2027.

Jaridar Legit.ng ta yi karin haske kan wasu 'yan siyasar Kano guda uku da ke ba Tinubu goyon baya mai karfi a kasa:

1. Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya taba zama gwamnan jihar Kano daga 2015 zuwa 2023. A yanzu shi ne shugaban jam'iyyar APC mai mulki ta kasa.

Ganduje, mai shekaru 74, ya ci gaba da kasancewa amintacce kuma na hannun daman Shugaba Tinubu kuma Tinubu ya san da hakan.

A lokuta da dama, shugaban kasar ya yaba wa Ganduje a matsayin ginshikin abokantaka, kuma shugaba mai rikon amana.

Yayin da ake fuskantar kalubalen tabarbarewar tattalin arziki da kuma korafe-korafen da ‘yan Najeriya ke yi, Ganduje ya jaddada cewa abokin nasa (Tinubu) ya na kan hanya madaidaiciya.

Kara karanta wannan

“An samu tsaro a Najeriya”: Ribadu ya fadi bambancin gwamnatin Tinubu da Buhari

Ana ganin, Abdullahi Ganduje zai taka muhimmiyar rawa a zaben 2027 mai zuwa domin ganin Tinubu ya samu nasarar yin tazarce.

2. Alhassan Doguwa

Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, dan jam'iyyar APC ne mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada daga jihar Kano.

Hon. Doguwa dai yana kare muradun Shugaba Tinubu tun kafin shugaban kasar ya ci zaben 2023.

Nunin goyon bayansa na baya-bayan nan ga shugaban kasar ya zo ne ta wata sanarwar manema labarai a ranar Juma’a, 4 ga Oktoba.

A cikin sanarwar, dan majalisar wakilan ya yi tir da kalaman Rabiu Kwankwaso, inda ya nace cewa Shugaba Tinubu na aza harsashin samar da Najeriya mai inganci da wadata.

A zaben 2027 mai zuwa, ana ganin karfin da Doguwa ya samu na zama shugaban masu rinjaye zai taimaka masa wajen tallata Tinubu da kyau.

3. Sanata Barau Jibrin

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

Sanata Barau Jibrin shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a yanzu tun bayan nadasa a 2023. Shi ne ssanata mai wakiltar Kano ta Arewa tun daga zaben 2015.

Tun a ranar 13 ga watan Yunin 2023 da aka amince da nadin Sanata Barau ba tare da hamayya ba a lokacin kaddamar da majalisar dattawa ta 10, ya zama babban jigo a zauren majalisar.

Jaridar Legit Hausa ta ruwaito Sanata Jibrin na ci gaba da karbar wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar sa ta APC. Ya na kara ci gaba da da'awar nemawa Tinubu mabiya.

A watan Satumba, Sanata Barau ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da Tinubu a kokarinsa na magance kalubalen zamantakewa da tattalin arzikin kasa.

A cewarsa sanatan, wahalar da ake fuskanta a halin yanzu matsala ce ta duniya baki daya don haka ba ta a Najeriya kadai ake cin kwakwa ba.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan siyasar Kudancin Najeriya da za su iya kalubalantar Tinubu a 2027

Ganduje zai tsaya takara a 2027?

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya nesanta kansa daga raɗe-raɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Abdullahi Ganduje, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya ce fastocin da ke yawo ba su da alaƙa da shi kuma ya yi zargin akwai hannun wasu ƴan Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.