Fubara Ya Lallasa Wike: Bakuwar Jam'iyya Ta Lashe Jujerun Ciyamomi 22 a Ribas

Fubara Ya Lallasa Wike: Bakuwar Jam'iyya Ta Lashe Jujerun Ciyamomi 22 a Ribas

  • Wata bakuwar jam'iyya da Gwamna Siminalayi Fubara ya tura mutanensa su yi takara a cikinta ta lashe kujerun ciyamomi 22 cikin 23 na Ribas
  • Babban jami’in zaben jihar, Mai shari’a Adolphus Enebeli, ya bayyana sakamakon zaben a Fatakwal a daren ranar Asabar
  • An rahoto cewa bayan Nyesom Wike ya kwace ikon kananan hukumomin na dan wani lokaci, Fubara ya yi amfani da dabara wajen lashe zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya dawo da ikon mulkin kananan hukumomi a hannunsa daga magabacinsa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Masu biyayya ga Fubara da suka fafata zabe a karkashin jam’iyyar Action Peoples Party (APP) sun samu nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 22 cikin 23.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yaki jami'an tsaro, APC da PDP, ya cinye komai a zaben kananan hukumomi

Fubara ya kwace ikon kananan hukumomin Ribas daga hannun Wike
Mutanen Fubara su lashe kujeru 22 cikin 23 na kananan hukumomin jihar Ribas. Hoto: @SimFubaraKSC, @GovWike
Asali: Facebook

Babban jami’in zaben jihar, Mai shari’a Adolphus Enebeli, ya bayyana sakamakon zaben a Fatakwal a daren ranar Asabar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya kwace ikon Ribas

Wike ya karbe ragamar mulkin kananan hukumomi na wani dan lokaci ne bayan da magoya bayansa suka lashe zaben da PDP ta gudanar a watan jiya.

Duk da haka, Fubara bai nuna karaya ba inda ya umurci magoya bayansa da su koma jam'iyyar APP domin tsayawa takara.

Mutanen Wike sun karaya da tasirin Fubara kan zaben ciyamomi inda suka ki shiga zaben tare da garzayawa kotu, amma gwamnan ya sha alwashin gudanar da zaben.

An samu tashin hankula a zaben

An gudanar da zaben ne cikin tashe-tashen hankula da suka biyo bayan janyewar ‘yan sanda da aka dauka domin bayar da tsaro, inda ake zargin akwai sa hannun Wike a janyewar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ja daga, ya ce zai iya rasa ransa saboda adalci a zaben gobe

Enebili ya ce za a sanar da sakamakon zaben Etche, karamar hukumar da ba a bayyana sakamakon ciyaman dinta ba a nan gaba kadan.

A halin da ake ciki, jam’iyyun PDP da APC a Ribas sun yi gargadi kan bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar.

Fubara ya dakile harin 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da tawagarsa sun dakile wani yunkuri na wasu 'yan sanda da suka je sace kayayyakin zaben ciyamomin jihar.

An rahoto cewa wasu 'yan sanda bisa jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar sun dura ofishin hukumar zabe domin sace kayayyakin amma Fubara ya dakile su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.