Dokubo Ya Yi Barazana ga Jirgin Rundunar Sojoji, Ya Caccaki Ministan Tinubu a Bidiyo

Dokubo Ya Yi Barazana ga Jirgin Rundunar Sojoji, Ya Caccaki Ministan Tinubu a Bidiyo

  • Fitaccen dan gwagwarmaya a yankin Neja Delta, Asari Dokubo ya gargadi rundunar sojoji da yan sanda a jihar Rivers
  • Dokubo ya yi gargadin ne bayan ganin jirgin sojoji mai saukar ungulu na shawagi a saman gidansa da ke jihar
  • Dan gwagwarmayar ya sha alwashin kado jiragen daga sama inda ya caccaki Ministan Abuja, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Tsohon shugaban tsageran Neja Delta, Asari Dokubo ya yi zazzafan gargadi ga rundunar sojoji.

Dokubo ya yi gargadin ne yayin da yake zargin jirgin sojoji na shawagi a gidansa a jiya Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.

Dokubo ya sha alwashin kado jirgin saman sojoji
Asari Dokubo ya caccaki Ministan Abuja, Nyesom Wike kan rikicin jihar Rivers. Hoto: Asari Dokubo.
Asali: Twitter

Rivers: Dokubo ya gargadi sojoji a Najeriya

Kara karanta wannan

"Ba na maganar 2027": Tinubu ya magantu kan zabe, ya fadi abin da ke gabansa a yanzu

Dan gwagwarmayar ya sha alwashin kado jirgin daga sama inda ya ce babu mai yi masa barazana a faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokubo ya ce wannan duka wani makirci ne na gwamnati da Nyesom Wike da magoya bayansa.

"Ina da karfin da zan kifar da su, babu yadda Najeriya za ta yi biyayya ga Wike, Rivers ba za ta bi Wike ba hala kabilar Ijaw."
"Wike ba kowa ba ne, ban taba jin tsoron mutuwa ba bare wani Wike, kullum neman ta nake yi."

- Asari Dokubo

Dokubo ya yi rantsuwa kan kado jirgin sama

Dokubo ya yi gargadin cewa bai kamata a zarge shi ba idan har aka kifar da jiragen masu saukar ungulu.

Ya ce ya rantse da Allah idan da ta fita sai ya kado jirgin saman sojoji da ke shawagi a saman gidansa ba tare da bata wani lokaci ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ja daga, ya ce zai iya rasa ransa saboda adalci a zaben gobe

Wike ya gargadi 'ya'yan Buhari kan filaye

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba 'ya'yan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasu yan siyasa wa'adin mako biyu.

Wike ya ba da wa'adin ne domin biyan kudin da ake binsu na filaye a yankin Maitama II saboda samun satifiket na mallakarsu.

Hukumar FCTA a birnin ita ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta yi barazanar kwace su idan ba a bi ka'idar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.