Ana Fargabar Jami'an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Kada Kuri'a, Sun Kwace Kayan Zaben
- Ana zargin jami'an tsaro da kansu sun kai farmaki kan masu zabe inda suka watsa su a jihar Rivers
- An tabbatar da cewa jami'an tsaron sun shiga harabar makarantar firamare ta Elakahia da tarwatsa masu zabe
- Hakan na zuwa ne yayin da ake gudanar da zaben ƙananan hukumomi a yau Asabar 5 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Ana fargabar jami'an tsaro sun tarwatsa masu gudanar da zabe a jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne a yau Asabar 5 ga watan Oktoban 2024 a makarantar firamare ta Elakahia da ke Port Harcourt.
Rivers: Ana zargin jami'an tsaro sun tarwatsa zaɓe
Channel TV ta wallafa wani bidiyo inda aka gano yadda wasu cikin kayan jami'an tsaro suka watsa masu zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zaben da ke zargin wadanda suka watsa taron jami'an tsaro ne sun koka kan yadda aka watsa masu barkonon tsohuwa.
Jami'an da ke gudanar da zaben daga hukumar INEC sun gama shiri domin fara zaben kafin aka watsa su.
An tarwatsa masu zaɓe da kwace kayansu
Jami'an tsaron da ake zargin sun shigo farfajiyar makarantar ne rike da makamai inda suka kori dukan mutane da ke ciki waje.
Daga bisani, an tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kwashe kayayyakin zaben da aka fama shirya su a wurin.
Daya daga cikin jami'an ya ci zarafin wani ma'aikacin wucin gadi na INEC inda ya ce masa ya cire rigar aikin da ke jikinsa.
"Zo nan wurin, ka cire wannan riga da ka saka ta INEC, mene ka ke yi a nan?"
- Cewar wata majiya
Zanga-zanga ta barke ana gudanar da zabe
Kun ji cewa magoya bayan ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun fito kan tituna domin nuna adawarsu da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a jihar Rivers.
Masu zanga-zangar sun buƙaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya bi umarnin kotu wanda ya hana a gudanar da zaɓen a jihar.
Zanga-zangar na zuwa ne yayin da mutane suka fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na ranar Asabar mai cike da cece-kuce.
Asali: Legit.ng