"An Kusa Daina Ganin Jar Hula": Jam'iyyar APC Ta Kara Rikita NNPP a Jihar Kano

"An Kusa Daina Ganin Jar Hula": Jam'iyyar APC Ta Kara Rikita NNPP a Jihar Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya karɓi wasu kusoshi da ƴan NNPP da sauka sauya sheka zuwa APC a Kano
  • Barau ya ce ƴaƴan NNPP na ci gaba da tururuwa zuwa APC saboda ayyukan da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi
  • A cewarsa, nan gaba kaɗan za a nemi jar hula watau alamar ƴan Kwankwasiyya a rasa a faɗin jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Ɗaruruwan mambobin jam'iyyar NNPP sun bar tafiyar Kwankwasiyya a Kano, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, shi ne ya karɓi masu sauya sheƙar ciki har da manyan jiga-jigan NNPP a ofishinsa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayyana abin da 'yan Najeriya za su yiwa APC a 2027

Sanata Barau I. Jibrin.
Sanata Barau ya karbi ɗaruruwan ƴan NNPP zuwa APC, ya ce jar hula ta gama zamani a Kano Hoto: @barauijibrin
Asali: Facebook

Wani babban jigo a NNPP, Garba Rama Rano da wasu manyan ƙusoshi na cikin waɗanda suka rungumi APC a wannan karon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wasu saƙonni haɗe da hotuna da Sanata Barau I. Jibrin ya wallafa a shafinsa na X.

'APC na ƙara samun karbuwa a Kano'

Da yake jawabi bayan karɓar masu sauya sheƙar, mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce nan ba da jimawa ba za a daina ganin masu jar hula a Kano.

Sanata Barau ya ce yadda ƴaƴan NNPP ke turuwa zuwa APC ciki har da shugabanni alama ce da ke nuna jam'iyyar na ƙara samun karɓuwa da goyon baya.

A cewarsa, duk da APC na tsagin adawa amma yadda ƴan Kwankwasiyya ke cire jar hula, suna dawowa cikinta ya kara nuna jam'iyyar na ƙara farin jini a Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun harbe shi ahmlahira a jihar Arewa

"Za mu kawar da jar hula" - Barau

"Zan ci gaba da karɓar ƴan NNPP da ke son dawowa APC, siyasa ta gaji haka domin idan kana cikin jam'uyya amma ba a shigowa cikinta lallai akwai matsala.
"APC ta zama abin sha'awa ga ƴaƴan NNPP saboda ɗumbin ayyukan alherin da gwamnatin Bola Tinubu take yi a Kano da ƙasa baki ɗaya, za mu ci gaba da karɓar ƴan NNPP da sauran ƴan siyasa ba ruwanmu da surutun wasu.
"Nan gaba za ku nemi mai jar hula, alamar Kwankwasiyya a Kano ku rasa, lokaci zai yi da nemo mai jar hula zai zama abu mai matuƙar wahala, nan ba da jimawa za mu kawo wurin."

- Barau I. Jibrin.

Kwankwaso ya hango makomar APC a 2027

A wani labarin kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki APC mai mulki a Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewa APC ta wahalar da ƴan Najeriya kuma za su sauya ta a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262