Gwamna Ya Ja Daga, Ya Ce Zai Iya Rasa Ransa Saboda Adalci a Zaben Gobe

Gwamna Ya Ja Daga, Ya Ce Zai Iya Rasa Ransa Saboda Adalci a Zaben Gobe

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya kafe kan lallai sai zaben kananan hukumomi ya gudana a gobe
  • A baya, kotun tarayya ta hana gudanar da zaben kananan hukumomin yayin da yan sanda su ka janye tsaro
  • Amma a ganawarsa da manema labarai a Ribas, gwamna Fubara ya ce babu gudu babu ja da baya game da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana cewa ba zai zuba idanu a aikata ba daidai ga jama'ar jihar Ribas ba.

Gwamnan ya ce a shirye ya ke ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da an yi wa jama'ar jiharsa adalci kamar yadda mai fafutukar nan, Martin Luther Kings ya yi.

Kara karanta wannan

An rikita Ribas, masu zanga zanga sun fusata, sun dunguma ofishin hukumar zabe

Sir Siminalayi Fubara
Gwamnan Ribas ya kafe kan zaben kananan hukumomin Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta tattaro cewa gwamna Fubara ya sha alwashin za a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar duk da janye yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dole a yi zabe gobe:" Gwamnan jihar Ribas

Gwamnan jihar Ribas ya jaddada cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar 5 Oktoba, 2024.

Matakin na zuwa ne bayan kotun tarayya ta haramta gudanar da zaben a gobe, sannan rundunar yan sandan kasar nan ta janye jami'anta daga bayar da tsaro.

Gwamna ya ce za su jajirce kan zaben Ribas

Gwamnatin jihar Ribas ta bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani yunkuri daga wasu mutane ko kungiyoyi na hana zaben kananan hukumomi a jihar ba.

"Za mu tabbatar da an gudanar da zabe, kuma za a rantsar da wadanda su ka yi nasara domin su kama aiki."

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun tunkari hedikwatar yan sanda da DSS kan zabe

- Gwamna Siminalayi Fubara

Masu zanga zanga sun rikita Ribas

A wani labarin kun ji cewa wasu mazauna Ribas sun gudanar da zanga-zanga inda su ka nuna goyon bayansu ga batun da gwamna Siminalayi Fubara ya sa a gaba.

Masu zanga Zangar sun nufi ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas, su ka nemi a tabbata an gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.