"Har Yanzu a Firgice Ka Ke": Doguwa Ya Mayarwa Kwankwaso Martani kan Kalamansa
- Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Tudun Wada/Doguwa a Kano ya mayarwa Rabiu Musa Kwankwaso martani
- Hon. Alhassan Doguwa ya ce har yanzu Kwankwaso a kidime yake bayan faduwa zaben 2023 a hannun Bola Tinubu
- Doguwa ya shawarci Kwankwaso ya mayar da hankali kan zaben 2027 inda za a yi masa ritaya gaba daya a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dan Majalisar Tarayya a jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya soki Sanata Rabiu Kwankwaso.
Alhassan Ado Doguwa ya mayar da martani kan kalaman Kwankwaso inda ya ke sukar gwamnatin Bola Tinubu.
2027: Ado Doguwa ya caccaki Kwankwaso
Dan Majalisar ya bayyana haka ne ga manema labarai a Kano a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Doguwa ya ce har yanzu Kwankwaso bai gama warkewa daga faduwar zaben da ya yi a 2023 ba.
Hon. Doguwa ya ce Kwankwaso ba shi da mutuncin da zai yi magana a madadin yan Arewa gaba daya.
"Tsohon gwamnan Kano har yanzu bai gama warwarewa ba bayan faduwa zaɓe a hannun Bola Tinubu a 2023."
"Shiyasa tun yanzu ya rikice inda ya ke babatu kan zaben 2027 mai zuwa."
- Alhassan Ado Doguwa
Ado Doguwa ya ba Kwankwaso shawara
Hon. Doguwa ya shawarci Kwankwaso ya mayar da hankali a 2027 da za a yi masa ritaya daga siyasa, The Guardian ta ruwaito.
Ya ce Bola Tinubu yana kokarin samar da abubuwan more rayuwa ga yan kasa saboda haka babu buƙatar dauke masa hankali.
Wannan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa yan Najeriya musamman yan Arewa sun gaji da mulkin Tinubu.
Kwankwaso ya fadi haka ne a jiya Alhamis 3 ga watan Oktoban 2024 inda ya ce yan kasar sun zaku a sake zaben domin kawar da Tinubu.
Kwankwaso ya magantu kan zama mataimakin Obi
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan yiwuwar zama mataimakin Peter Obi a zaben 2027.
Kwankwaso ya ce shi ba sa'an Obi ba ne a siyasa da kuma ilimi sai dai ya ce hakan ba matsala ba ne a wurinsa idan za a yi gaskiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng