‘Yan APC Maƙiya Talaka ne,’ Kwankwaso Ya Kawo Mafita da Ya Illata Jam'iyyar

‘Yan APC Maƙiya Talaka ne,’ Kwankwaso Ya Kawo Mafita da Ya Illata Jam'iyyar

  • Jagoran NNPP a Najeriya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga yan Najeriya kan shigowa tafiyarsu domin kawo cigaba
  • Sanata Rabi'u Kwankwaso ya ce sauya sheka da ake yi a Kano alama ce da ke nuna Abba Kabir Yusuf na aiki yadda ya kamata
  • Legit ta tattauna da wani mazaunin Kano domin jin yadda yake ga za a karbi maganar da Kwankwaso ya kawo ta shiga NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga al'umma kan shiga tafiyar NNPP domin kawo saukin rayuwa.

Hakan na zuwa ne yayin da yan siyasa suka yawaita sauya sheka a jihar Kano a kwanan nan musamman saboda zaben kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

'Za mu fitar da taruraro a kowane gida,' Kwankwaso ya yi albishir ga talakawa

Kwankwaso
Kwankwaso ya yi kira a shiga NNPP. Hot: Rabi'u Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanin da Rabi'u Kwankwaso ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya karbi yan APC zuwa NNPP

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi tulin yan jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a jihar Kano.

Legit ta ruwaito ruwaito cewa mutanen sun fito ne daga kananan hukumomin Dala, Kiru da Gwale a jihar Kano.

Jam'iyyar APC ba ta son talaka inji Kwankwaso

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya ce halin da ake ciki na wahalar rayuwa alama ce da ake nuna cewa APC ba tana kin talaka ya samu sauki.

Rabi'u Kwankwaso ya ce kuma babu wata alama da ke nuna cewa APC za ta sauya hali domin saukakawa talakawan Najeriya.

Kwankwaso ya kawo mafita a Najeriya

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa sauya sheka da ake zuwa NNPP a Kano alama ce da ke nuna Abba Kabir Yusuf yana aiki sosai.

Kara karanta wannan

"Har yanzu a firgice ka ke": Doguwa ya mayarwa Kwankwaso martani kan kalamansa

Jagoran NNPP ya ce kofa a bude take ga duk wanda yake son shiga tafiyar NNPP domin su hadu su kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Legit ta tattauna da Musa Adamu Musa

Wani mazaunin Kano, Musa Adamu Musa ya zantawa Legit cewa ba lallai kowa ya karbi maganar Kwankwaso ba.

Sai dai duk da haka ya ce halin kuncin rayuwa zai iya saka mutane da yawa shiga tafiyar Kwanwaso domin talakwa sun fi tsanmanin sauki a wajensa a kan APC.

Abba ya raba kayan karatu kyauta a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya mika kayan karatu na miliyoyin kudi a makarantun Kano domin bunkasa ilimi.

Abba Kabir Yusuf ya ce suna mayar da hankali kan ilimi ne kasancewar gwamnatin Abdullahi Ganduje ba ta ba shi muhimmanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng