Masu Zanga Zanga Sun Tunkari Hedikwatar Yan Sanda da DSS kan Zabe

Masu Zanga Zanga Sun Tunkari Hedikwatar Yan Sanda da DSS kan Zabe

  • Matasan PDP sun gudanar da zanga zangar adawa da zaben kananan hukumomi da gwamnatin Siminalayi Fubara za ta yi
  • Tarin matasan sun tunkari hedikwatar yan sanda da ofishin DSS na jihar domin nuna kukansu kan neman hana zaben gudana
  • A ranar Asabar gwamnatin Rivers za ta gudanar da zaben kananan hukumomi amma kotu ta ba da umarnin dakatar da shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Matasan jam'iyyar PDP sun jagoranci zanga zanga domin nuna fushi kan shirin zaben kananan hukumomi a Rivers.

Gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu makawa kan gudanar da zaben a ranar Asabar duk da cewa kotu ta bukaci ya dakata.

Kara karanta wannan

PDP da APC sun hada kai domin kalubalantar matakin gwamna kan zabe

Zanga zanga
Matasan PDP sun yi zanga zanga a Rivers. Hoto: Kola Sulaimon (An yi amfani da hoton ne domin buga misali)
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa masu zanga zangar sun bukaci jami'an tsaro su nisanci zaben da gwamnatin za ta gudanar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan PDP sun yi zanga zanga a Rivers

Matasan jam'iyyar PDP sun jagoranci zanga zangar adawa da zaben kananan hukumomi a jihar Rivers.

Daruruwan matasan sun ce abin bakin ciki ne yadda kotu ta hana zaben amma gwamna Fubara ya dage sai ya yi.

Wasu matasa sun tunkari hedikwatar yan sanda

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa matasa masu zanga zangar sun tunkari hedikwatar yan sandan Rivers da ofishin DSS na jihar.

Wani daga cikin matasan, John Amadi ya bukaci jami'an tsaro su kauracewa zaben kamar yadda kotu ta umarce su.

Jami'an tsaro sun yi wa matasan jawabi

Jami'an tsaro da suka karbi matasan sun bukace su da su guji daukar doka a hannu duk halin da za a shiga.

Kara karanta wannan

Nasarawa: NASIEC ta shirya gudanar da zaben ciyamomi, an fitar da jadawali

A yanzu haka dai hukumar zabe ta jihar Rivers ta ce ba makawa a kan zaben kananan hukumomi a jihar duk da umarnin kotu.

Jam'iyyu sun yi wa gwamnan Rivers taron dangi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers na fuskantar matsala daga jam'iyyun PDP da APC kan zaben ƙananan hukumomi.

Jam'iyyun guda biyu sun kalubalanci gwamnan kan shirin gudanar da zaben a ranar 5 ga watan Oktoban 2024 duk da hukuncin kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng