Na Kusa da Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Yi Garambawul a Majalisar Ministoci

Na Kusa da Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Yi Garambawul a Majalisar Ministoci

  • Yayin da ake ta yada jita-jitar cewa Bola Tinubu zai yi garambawul a mukaman Ministoci, jigon APC ya yi magana
  • Barista Daniel Bwala ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri su bar Tinubu ya yi abin da ya dace a lokacin da yake so
  • Bwala ya ce kafofin sadarwa ne suka kirkiri labarin kuma sun samu abin da suke so na tsawon kwanaki kan rahoton

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Barista Daniel Bwala ya yi magana kan rade-radin yin garambawul a majalisar Ministocin tarayya.

Bwala ya ce ya kamata yan Najeriya su yi hakuri shugaba Bola Tinubu zai rusa Ministocin a lokacin da ya dace.

Kara karanta wannan

'Ko shekaru 100 ka ba Tinubu bai san yadda zai yi da Najeriya ba'

Bwala ya yi magana kan garambawul na Ministoci da Tinubu zai yi
Daniel Bwala ya bukaci yan Najeriya su ba Bola Tinubu lokaci kan garambawul. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Daniel Bwala.
Asali: Twitter

Bwala ya magantu kan rusa Ministocin Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin wani bidiyo da Tashar Channels TV ta yi hira da Bwala a daren jiya Laraba 2 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya ce shugaban kasa zai yi garambawul din ne a lokacin da ya ga ya dace ko lokacin da ya ke so.

Tsohon jagoran na PDP ya ce kafofin sadarwa ne suka kirkiri labarin yin garambawul din kuma sun yi nasara.

Bwala ya roki a ba Tinubu lokaci kan Ministoci

"Shugaba Tinubu zai yi hakan ne lokacin da yake so, abu mai muhimmanci shi ne zai yi abin da ya dace wurin auna kokarin Ministocin."
"Duk wani Minista da ya gaza kai wa inda ake so bayan gwaji da manhajar KPI Tinubu zai sani."
"Kafafen sadarwa suna son a yi garambawul shi ya sa suka kirkiri labarin kuma ya watsu a ko ina, amma ina son yan Najeriya da su kara hakuri kan haka."

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

- Daniel Bwala

Halin kunci: Tinubu ya yabawa gwamnonin Najeriya

Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya ba yan Najeriya tabbacin yana daukar matakai masu muhimmanci domin rage tsadar rayuwa.

Mai girma Tinubu ya yabawa wasu gwamnonin Arewacin Najeriya kan kokarin da suka yi wurin rungumar harkokin noma.

Shugaban ya kuma roki sauran gwamnonin jihohin Najeriya da su ba da karfi da kuma hadin kai ga Gwamnatin Tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.