Tajudeen Abbas: Shugaban Majalisa Ya Bayyana Ubangidansa a Siyasa

Tajudeen Abbas: Shugaban Majalisa Ya Bayyana Ubangidansa a Siyasa

  • Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya yi magana kan irin gwagwarmaya da faɗi tashin da ya yi a rayuwa
  • Tajudeen Abbas ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin mutane ƙalilan a ƙasar nan waɗanda ba su da ubangida a siyasance
  • Ya ce babu wanda ya taɓa ɗaukar nauyinsa domin a zaɓe shi ko ya zarce, ya ce jama'a ne suke yabawa da aikin da yake yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai ta 10, Tajudeen Abbas ya yi magana kan ubangidan da yake da shi a siyasa.

Shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin ƴan siyasan da ba su da ubangida a siyasa.

Tajudeen Abbas bai da ubangida a siyasa
Tajudeen Abbas ya ce bai da ubangida a siyasa Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Tajudeen Abbas ya tattauna da ɗalibai

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaba Tinubu ya yi magana kan farashin kayan abinci, ya faɗi mafita

Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da zaɓabbun ɗaliban makarantun sakandare na gwamnati da ya tattauna da su, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tattauna da ɗaliban ne a yayin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai, wanda kuma ya yi daidai da cikarsa shekara 59 da haihuwa.

Tajudeen Abbas wanda ya buƙaci matasan Najeriya su yi imani da kansu maimakon dogaro da iyayensu, ya bayyana yadda ya samu ɗaukakarsa ga ɗaliban tare da sauran ƴan Najeriya da suka halarci taron.

"Ba ni da ubangida a siyasa", Tajudeen Abbas

"A lokacin da na kai shekara 19, na riga na mallaki gidana. Ina da gidana a shekara 19, da gumina na gina gidana. Ban taɓa buƙatar gudunmawa ko sau ɗaya daga ƴan uwana ba."

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yancin kai: Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya, an samu bayanai

"Ko da na shiga siyasa, tabbas ina ɗaya daga cikin ƴan ƙalilan da za a iya samu a ƙasar nan waɗanda ba su da ubangida a siyasa."
"Babu wanda ya taɓa goyon bayana ko ya ɗauki nauyina, babu shi. Ban ɓoye a ƙarƙashin inuwar kowa domi a zaɓe ni ko a sake zaɓe na ba."
"Na yarda da kaina kuma na yi wa jama'a hidima. Sun yaba kuma suka ci gaba da sake zaɓena."

- Tajudeen Abbas

Ƴan majalisa sun ja daga da Tinubu kan Abbas

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar wakilai sun nuna kin amincewa da lambar girma da Bola Tinubu zai ba shugabansu.

Shugaban kasa ya zaɓi shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen domin ba shi lambar yabo ta CFR a ranar murnar samun 'yancin kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng