Gwamna Ya Bayar da Hutu a Ranakun Alhamis da Juma'a a Jiharsa, Bayanai Sun Fito
- Gwamnan jihar Ribas ya ayyana Alhamis da Jumu'a a matsayin ranakun hutu domin ba ma'aikata damar komawa yankunansu
- Siminalayi Fubara ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin mutane su koma gida su kaɗa kuri'unsu a zaɓen kananan hukumomi
- Ya kuma sanar da taƙaita zirga-zirgar ababen hawa daga tsakar daren ranar Juma'a zuwa ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ayyana Alhamis da Juma'a, 3 da 4 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranakun hutu.
Gwamna Fubara ya ba da hutun kwanaki biyun ne domin bai wa ma'aikata damar komawa yankunansu domin kaɗa kuri'a a zaɓen kananan hukumomin da za a yi.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar zaɓen jihar Ribar ta shirya gudanar da zaɓen kananan hukumomi ranar Asabar mai zuwa, 5 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya taƙaita zirga-zirga a Ribas
Gwamnan ya kuma sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa daga tsakar daren ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba zuwa karfe 5:00 na yamma a ranar zaben.
Siminalayi Fubara ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi kai tsaye ga mazauna Ribas daga gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Laraba.
Ya ce za a yi zaɓen ne bayan ƙarewar wa'adin ciyamomi da kansiloli a faɗin kananan hukumomi 23 ranar 17 ga watan Yuni, 2024, rahoton Channels tv.
Dalilin shirya zaɓen ƙananan hukumomi
A cewarsa, tun bayan karewar wa'adin ciyamomin, ya naɗa kantomomin da za su kula da harkokin kananan hukumomin gabanin hukumar RSIEC ta shirya zaɓe.
Fubara ya ce hakan ya biyo bayan hukuncin kotun ƙoli na bai wa kananann hukumomi cikakkiyar damar cin gashin kai tare da umarnin daina tura kason waɗanda ba su da zaɓaɓɓun ciyamomi.
Gwamnan ya ce bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa baki, an tsawaita wa'adin fara aikin dokar da watanni uku wanda zai kare ranar 31 ga watan Oktoba.
"Saboda haka mun ba da hutun ranakun Alhamis da Juma'a, 3 da 4 ga watan Oktoba, 2024 don mutane su koma yankunansu su kaɗa kuri'a,' in ji Fubara.
Gwamnan Adamawa ya roki Wike da Fubara
A wani labarin kuma gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers da ake fama da ita tun 2023.
Gwamna Fintiri ya roƙi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da su kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng