Majalisa Ta Yi Amai Ta Lashe kan Dakatar da Mambobinta, Ta Fadi Dalili

Majalisa Ta Yi Amai Ta Lashe kan Dakatar da Mambobinta, Ta Fadi Dalili

  • Majalisar jihar Edo ta yi amai ta lashe bayan dakatar da mambobinta guda biyu a watan Mayun 2024 da ta wuce
  • Majalisar ta janye dakatarwar bayan wata hudu da dakatar da Donald Okogbe da Adeh Isibor kan wasu zarge-zarge
  • Tun farko, Majalisar da dakatar da 'ya 'yanta kafin daga bisani ta janye wannan matakin nata bayan wata daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Majalisar jihar Edo ta sanar da janye dakatarwar da ta yi wa mambobinta guda biyu.

Majalisar ta tabbatar da dawo da sauran mambobinta guda biyu, Donald Okogbe da Adeh Isibor daga dakatarwar na tsawon watanni biyar.

Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa mambobinta
Majalisar jihar Edo ta dawo da mambobinta da ta dakatar a watan Mayu. Hoto: Edo State House of Assembly.
Asali: Facebook

Majalisar Edo ta dawo da mambobinta 2

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Punch ta ruwaito cewa Majalisar ta dauki matakin ne a yau Laraba 2 ga watan Oktoban 2024 yayin zamanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta tabbatar a watan Mayun 2024 Majalisar ta dakatar da mambobinta guda uku kan zargin tsige kakakinta da mukarrabansa.

Daga cikin wadanda aka dakatar din akwai Bright Iyamu da Donald Okogbe da kuma Adeh Isibor.

Sai dai an kira Iyamu a watan Yunin 2024 bayan ya yi nadamar abin da ya aikata kamar yadda shugaban Majalisar, Blessing Agbebaku ya tabbatar.

Shugaban Majalisa ta taya zababben gwamna murna

Shugaban Majalisar, Hon. Blessing Agbebaku shi ya tabbatar da janye takunkumin kan yan Majalisar da aka dakatar, cewar Tribune.

Daga bisani, Agbebaku ya taya sabon zababben gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Monday Okpebholo murnar samun nasara a zabe.

Rigima ta kaure kan nadin sabon sarki

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Kun ji cewa zanga-zanga ta barke yayin da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya tabbatar da nadin sabon sarki da ake zargi an yi ba tare da bin ka'ida ba.

Dattawa da shugabannin yankin Okpella a jihar sun yi fatali na nadin Lukman Akemokhue a matsayin sarki inda suka ce gwamnan ya yi shisshigi.

Gwamnan ya tabbatar da nadin tare da mika takardar mukamin a ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.