Jiga Jigan NNPP a Kano da Arewa da Suka Tsallake Kwankwaso Zuwa APC

Jiga Jigan NNPP a Kano da Arewa da Suka Tsallake Kwankwaso Zuwa APC

A duniyar siyasa, ya halatta mutum ya sauya sheka daga jam'iyyar da ya ke zuwa wata domin inganta siyasarsa ko saboda wasu bukatu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A jihar Kano da NNPP ke mulki, ta rasa jiga-jiganta zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kusoshin NNPP da suka watsar da ita zuwa APC a Arewacin Najeriya
Jerin jiga-jigan NNPP a Kano da Arewa da suka sauya sheka zuwa APC. Hoto: All Progressives Congress, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau ya karbi jiga-jigai da dama daga Kano da ma Arewacin Najeriya zuwa APC.

Legit Hausa ta bankado wadanda suka bar NNPP da Rabiu Kwankwaso ke jagoranta zuwa APC da Abdullahi Ganduje ke shugabanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sani Dambo

A watan Sarumbar 2024, Sani Dambo ya ajiye mukaminsa na hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren zuba hannun jari.

Kara karanta wannan

"An yiwa ƙasa addu'a": Tinubu ya haɗu da tsofaffin shugabanni 2 da sarki a masallacin Jumu'a

Sanata Barau Jibrin ya karbi Dambo da kuma wani jigon NNPP, Rabiu Durun zuwa jam'iyyar APC.

2. Abdulrahman Mai Kadama

Abdulrahman Mai Kadama shi ma ya watsar da mukaminsa na hadimin Abba Kabir a bangaren koyan sana'o'i a watan Agustan 2024.

Kamar Dambo, shi ma Mai Kadama ya fice zuwa APC mai mulkin Najeriya bayan watsar da NNPP.

3. Rufai Ahmed Alkali

Tsohon shugaban jam'iyyar NNPP, Rufai Ahmed Alkali ya yi murabus daga shugabancinta inda ya koma APC a karshen shekarar 2023.

4. Sulaiman Hunkuyi

Tsohon Sanata a jihar Kaduna, Sulaiman Hunkuyi da tsohon babban sakataren hukumar NHRC, Ben Angwe sun koma APC.

Shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje shi ya tarbi sababbin tuban a sakatariyar APC da ke Abuja.

5. Mohammed Garba Isimbabi

A watan Agustan 2024, Isimbabi da ke wakiltar Toto/Gadabuke a Majalisar jihar Nassarawa ya watsar da jam'iyyarsa ta NNPP zuwa APC mai mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Abba ya yiwa Ganduje illa a siyasa, tulin 'yan APC sun sauya sheka a mahaifarsa

6. Musa Abubakar

Har ila yau, a jihar Nasarawa, dan Majalisar jihar da ke wakiltar Doma ta Kudu, Musa Abubakar Ibrahim ya fice daga NNPP.

Daruruwan mambobin APC sun koma PDP a Ondo

Kun ji cewa jam'iyyar PDP a jihar Ondo ta yi murnar karɓar mambobin jam'iyyar APC sama da 200 waɗanda suka raba gari da ita.

Masu sauya sheƙar dai sun yi hujja da rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar APC wajen canza gidan.

Ana kallon wannan guguwar sauya sheƙar a matsayin babban cigaba ga PDP gabanin zaɓen gwamna a Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.