Halin da Ɗan Takarar Gwamna Ke ciki bayan Shekaru 3 da Sace Shi, an Samu Cigaba

Halin da Ɗan Takarar Gwamna Ke ciki bayan Shekaru 3 da Sace Shi, an Samu Cigaba

  • A ranar 18 ga watan Satumbar 2021 aka sace dan takarar gwamna a jam'iyyar LP a jihar Anambra, Obiora Agbasimalo
  • Agbasimalo a yanzu haka ya shafe shekaru uku kenan babu labarinsa ko kuma wani bayani game da halin da ya ke ciki
  • Lamarin ya faru ne yayin da dan takarar ke kamfe a kokarin neman mulki a Luli da ke karamar hukumar Ihiala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Dan takarar gwamna a jam'iyyar LP ya shafe shekaru uku babu labarinsa bayan yan bindiga sun sace shi.

Obiora Agbasimalo ya nemi takarar gwamna a zaben 2021 a jihar Anambra da aka gudanar da Gwamna Charles Soludo ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Har yanzu dan takarar gwamna a LP da aka sace yana tsare ba labari
Bayan yan bindiga sun sace dan takarar gwamna shekaru 3 da suka wuce, har yanzu babu labari. Hoto: Obiora Agbasimalo.
Asali: Facebook

Anambra: Yadda aka sace dan takarar gwamna

Premium Times ta ce an sace Agbasimalo ne a ranar 18 ga watan Satumbar 2021 kasa da watanni biyu kafin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yau shekaru uku kenan babu labarin Agbasimalo wanda ya ajiye aikinsa na banki domin neman takara.

Lamarin ya faru ne a Lilu da ke karamar hukumar Ihiala a jihar yayin da ya je kamfe a Azhia.

An sace tsohon ma'aikacin bankin ne da daya daga cikin yan sanda da ke tare da shi a cikin tawagar.

Halin da ake ciki kan sace dan takara

Tun farko, jam'iyyar LP ta bukaci iyalan dan takarar kada su kai korafi wurin yan sanda saboda yan bindigan sun yi alkawarin sake shi bayan zaben gwamna a lokacin.

Sai dai hakan bai faru ba inda iyalan suka yi korafi a ofishin hukumar DSS wanda daga bisani aka yi sanadin kama mutane biyu da ake zargi.

Kara karanta wannan

Ana zargin an dauki hayar 'yan bindiga, sun kashe dan takarar PDP a Kaduna

Gwamnan Anambra zai fara biyan albashin N70,000

Kun ji cewa yayin da rayuwa ke kara tsada duk kwanan duniya a Najeriya, Gwamna Charles Soludo zai biya sabon albashi.

Gwamna Soludo ya amince da fara biyan sabon mafi karancin albashin N70,000 a karshen wannan watan Oktoba.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin saukakawa ma'aikata tare da kuma samar da ilimi kyauta ga daliban sakandare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.