Shugabancin PDP: Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Iya Tarwatsa Jam'iyyar

Shugabancin PDP: Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Iya Tarwatsa Jam'iyyar

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya yi tsokaci kan rikicin da ake yi kan kujerar shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa
  • Mutfwang ya buƙaci 'yan PDP su guji yin kalamai masu kawo rarrabuwar kai waɗanda za su iya kawo rashin zaman lafiya a jam'iyyar
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an warware rikice-rikicen da suka dabaibaye jam'iyyar hamayyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya yi magana kan taƙaddamar da ake yi kan kujerar shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.

Gwamna Mutfwang ya buƙaci da a kwantar da hankula a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan kujerar shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gano matsalolin da suka hana Najeriya samun ci gaba

Muftwang ya magantu kan rikicin PDP
Gwamna Mutfwang ya bukaci mambobin PDP su daina kalaman da za su kawo rarrabuwar kai Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Twitter

Wane gargaɗi gwamna ya yi ga ƴaƴan PDP?

Gwamnan ya yi gargaɗin cewa rashin tauna kalaman da wasu ƴaƴan jam'iyyar ke yi ba zai haifar da komai ba face kawo tangarɗa ga zaman lafiya da haɗin kan jam'iyyar a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mutfwang ya buƙaci mambobin PDP da su daina yin kalamai waɗanda za su kawo rarrabuwar kai, rahoton jaridar Businessday ya tabbatar.

Gwamnan ya kuma nuna godiyarsa ga mambobin PDP da shugabanninta musamman daga yankin Arewa ta Tsakiya kan yadda suka tsaya tsayin daka wajen yi wa jam'iyyar biyayya.

Ina aka kwana kan rikicin PDP?

Mutfwang ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na aiki tuƙuru domin ganin sun warware rikice-rikicen da suka addabi PDP ciki har da batun shugabancin jam'iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Dauda ya bayyana matsayarsa kan sulhu da 'yan bindiga

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙari wajen ganin PDP ta zama jam'iyyar da ke kan gaba wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da shugabanci mai kyau.

Wike ya gargaɗi ƴan jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙara rikirkita jam'iyyar PDP kan rikicin siyasar da har yanzu ya ƙi ƙarewa a jihar Ribas.

Wike ya bayyana cewa ya fi ƙarfin duk wanda zai shiga takun saƙa ko ya yake shi, yana mai cewa dukkan masu adawa da shi ba za su iya galaba a kansa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng