Kafin Shiga Ofis, Atiku Ya Kawo Gyara a Tsarin Mulki na Shugaban Kasa da Gwamnoni

Kafin Shiga Ofis, Atiku Ya Kawo Gyara a Tsarin Mulki na Shugaban Kasa da Gwamnoni

  • Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ba da shawara kan shugabanci a Najeriya
  • Atiku ya ce ya kamata shugaban kasa da gwamnoni su yi wa'adi daya kacal na shekaru shida sabanin tsarin yanzu
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma bukaci damawa da dukan yankuna shida na Najeriya daga Arewa zuwa Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci sauyin tsarin mulki na shugaban kasa da gwamnoni.

Atiku ya rubuta wasika ga Majalisar Tarayya domin ba shugaban kasa damar yin wa'adi daya na shekaru shida kacal.

Atiku ya ba da shawara kan tsarin shugabanci a Najeriya
Atiku Abubakar ya bukaci ba shugaban kasa da gwamnoni wa'adi 1 na shekaru 6 a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Atiku ya ba da shawara kan tsarin mulki

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci juya shugabancin tsakanin yankin Kudu zuwa Arewa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

"Kai ka jawo tsadar rayuwa": 'Dan majalisa ya cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bukaci Majalisar da ta yi gyara a sashe na 132 inda ya ba da shawara kan mafi karanci shedar karatu ga yan takara.

"Ya kamata a rika juya ofishin shugaban kasa zuwa duka yankuna shida na Najeriya kuma ya zama wa'adi daya na shekaru shida."
"Duba da karamin sashe na 1, ya kamata shugaban kasa ya bar ofishi bayan kammala shekaru shida"

- Atiku Abubakar

Atiku ya bukaci gyara a neman takara

Atiku ya bukaci sauya satifiket na sakandare a matsayin mafi karancin shedar karatu na neman shugabanci a Najeriya.

Ya ce ya kamata a ce shedar karatu na 'Difloma' ya zama mafi karancin sheda na neman wani mukami a Najeriya.

Har ila yau, Atiku ya ba da shawara kan ba jam'iyyun siyasa karfi wurin zaben dan takararsu a zabe.

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan NLC

Kara karanta wannan

"Da wuya a magance rashin tsaro:" Obasanjo ya gano abin da ke barazana ga kasa

Kun ji cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu saboda matakin da ta dauka kan NLC.

Atiku Abubakar ya ce yadda gwamnatin kasar nan ke kokarin murkushe kungiyoyin kwadago na nuna tsagwaron zalunci ne da abin takaici.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma buga misali da yadda aka kama wani dan jarida, inda bayan an sake shi aka ce kuskure ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.