APC, PDP Sun Sha Kashi: APGA Ta Lashe Zaben Duka Ciyamomi a Kudancin Najeriya
- Jam'iyyun adawa a jihar Anambra da suka hada da APC, PDP sun tashi a tutar babu yayin da aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar
- Hukumar zaben jihar Anambra (ANSIEC) ta sanar da cewa jam'iyya mai mulki ta APGA ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da na kansiloli
- A ranar Lahadi, 29 ga watan Satumbar 2024 ANSIEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 21 da na gundumomi 326 na jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Jam’iyyar APGA mai mulki a jihar Anambra ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da na kansiloli.
An ce jam'iyyun adawa irinsu PDP, APC da sauransu ba su iya samun ko da kujera daya ta ciyaman ko kansila a zaben kananan hukumomin Anambra ba.
Anambra: An yi zaben ciyamomi 21
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 21 da kuma gundumomi 326 na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin labaran ya kuma ruwaito cewa mace daya ce kawai ta samu damar lashe kujerar shugabar karamar hukuma a zaben.
Genevieve Osakwe, shugabar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Anambra (ANSIEC), ta bayyana sakamakon zaben a ofishin hukumar da ke Awka a daren Lahadi.
APGA ta lashe dukkanin kujeru
Misis Osakwe ta ce jam’iyyar APGA ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 21 da na kansiloli a fadin kananan hukumomin jihar.
“An sanar da dukkanin ƙuri'un da jam’iyyu suka samu daga rumfunan zabe a jiya, yanzu mun zo nan ne domin tabbatar da sakamakon kamar yadda aka tattara.
"An gudanar da zabe a dukkanin rumfunan zabe da ke fadin Anambra ranar Asabar, kuma an yi zabe cikin 'yanci, adalci da gaskiya."
- Inji shugabar ANSIEC.
Premium Times ta rahoto Osakwe ta yabawa al’ummar Anambra bisa yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’unsu.
Anambra: Za a fara biyan N70,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya sanar da cewa zai fara biyan ma'aikatan jiharsa sabon albashin N70,0000 a watan Oktoba.
Gwamna Soludo ya yi albishir din ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabanni makarantun firamare da sakandare na gwamnati da ke a fadin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng