Gwamnan PDP Ya Tsorata, Ya Nemi Alfarma wajen Nyesom Wike

Gwamnan PDP Ya Tsorata, Ya Nemi Alfarma wajen Nyesom Wike

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya miƙa ƙoƙon bararsa ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
  • Seyi Makinde ya buƙaci Wike da ya yi haƙuri ya kai zuciya nesa ka da ya kunno wuta a jiharsa a Oyo
  • Gwamna Makinde ya yabawa Wike bisa ayyukan da ya yi a jihar Rivers lokacin da yake kan muƙamin gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya roƙi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da ka da ya kunno wuta a jihar Oyo.

Kwanakin baya a wajen wani taro, Wike ya yi barazanar haifar da rikicin siyasa a jihohin gwamnonin PDP masu goyon bayan gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara.

Kara karanta wannan

"Na fi ƙarfinku," Ministan Tinubu ya ƙara ta da Hazo, ya yiwa wasu gwamnoni shaguɓe

Makinde ya roki Wike
Seyi Makinde ya bukaci Wike ka da ya kunno wuta a Oyo Hoto: Seyi Makinde, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Gwamna Makinde, a wajen liyafar da ƙungiyar ƴan ƙabilar Ijaw suka shiryawa Wike a ranar Asabar, ya roƙi ministan da ka da ya kunno wuta a jihar Oyo, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Makinde ya yabawa Wike

Gwamna Makinde ya yabawa tsohon gwamnan na jihar Rivers kan ababen more rayuwa da ya samar a jihar, inda ya ce ministan ya yiwa al’ummarsa aiki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

“Na zo daga Oyo domin na taya ɗan uwana kuma wanda ake karramawa a yau (Nyesom Wike) murna."
"Lokacin da na zo Rivers (ranar Juma’a) na shaida masa cewa na zo da zaman lafiya saboda ya riƙa taƙama da cewa zai kunno wuta a wasu jihohin. Na ce masa don Allah kar a kunna wuta a jihar Oyo."
"Bari na faɗa a madadin sauran takwarorina gwamnoni da gwamnonin da suka gabata a nan cewa ka yiwa al’ummarka aiki, kuma tun da na zo na ga ayyukan da aka yi a tsawon shekaru takwas da ka yi a gwamna."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamnan PDP ya ba Wike da Gwamna Fubara shawara

- Gwamna Seyi Makinde

Gwamna ya ba Wike da Fubara shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Gwamna Fintiri ya roƙi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da su kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng