"Na Fi Karfinku," Ministan Tinubu Ya Kara Ta da Hazo, Ya Yiwa Wasu Gwamnoni Shaguɓe
- Nyesom Wike ya ƙalubalanci dukkan waɗanda ke ganin suna faɗa da shi, ya ce ko sun haɗa kai ba za su taba cin nasara a kansa ba
- Ministan babban birnin tarayya ya kuma waiwayi gwamnonin PDP, inda ya ce tun farko ya gargaɗe su kar su sa hannu a rigimar siyasar Ribas
- Wike ya yi wannan furucin ne a wurin liyafar da ƴan kabilar Ijaw suka shirya masa a Fatakwal ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙara rikirkita jam'iyyar PDP kan rikicin siyasar da har yanzu ya ƙi ƙarewa a jihar Ribas.
Wike ya bayyana cewa ya fi ƙarfin duk wanda zai shiga takun saƙa ko ya yake shi, yana mai cewa dukkan masu adawa da shi ba za su iya cin galaba a kansa ba.
Ministan ya kuma musanta raɗe-raɗin ƴan ƙabilar Ijawa sun juya masa baya a rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ya fito daga kabilar, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya yi wannan furuci ne a wurin liyafar da ƴan ƙabilar Ijawa suka shirya domin karrama shi a Fatakwal, babban birnin Ribas jiya Asabar.
Ministan Abuja ya musanta raba gari da Ijaw
Mista Wike ya ce ya zabi ya maida Fubara magajinsa duk da hakan ya saɓawa ra'ayin wasu 'yan kabilar Ijaw a zaɓen 2023.
“Ba gaskiya ba ne cewa mutanen Ijaw suna fada da ni, uba na iya haifar 'ya'ya 12, ɗaya ya zama zakka ya zama ɗan fashi.
"Mutanen da ke shiga gidan talabijin suna zagi na, ina suke lokacin da muka maida ɗan Ijaw ya zama gwamna?"
"Babu wanda ke faɗa da ni, na fi karfin a sa ƙafar wando ɗaya da ni, duk waɗannan mutanen da kuke gani idan suka haɗa kai ba za su iya ja da ni ba."
- Nyesom Wike.
Wike ya yi shagube ga gwamnonin PDP
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya taɓo gwamnonin PDP waɗanda ya yiwa barazanar kunno masu wuta idan suka tsoma baki a rikicin Ribas.
The Nation ta ruwaito Wike na cewa:
"Na faɗa masu idan suka sa hannu a sha'anin Ribas wuta za ta ƙona su, ga shi har sun fara kokawa, maimakon su maida hankali kan yadda za su ci zaɓe a jihohinsu, sun koma yin taruka a Taraba da Enugu, wa ya faɗi yanzu?"
Ya gargadi ‘yan siyasa da ke wajen jihar da su guji shiga harkokin siyasar Jihar Ribas, inda ya ce “Jihar Ribas ta musamman ce a gare ni.
Wike ya gana da ƴan BoT a Abuja
A wani rahoton kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya gana da ƴan majalisar amintattu na PDP (BoT) a daren ranar Talata, 17 ga watan Satumba 2024.
Legit Hausa ta fahimci cewa wannan taro wani wani ɓangare ne a yunƙurin BoT na kawo ƙarshen rigimar siyasar da ta dabaibaye jihar Ribas.
Asali: Legit.ng