"Wa Ka Taba Ginawa": Tsohon Gwamna ga Yaronsa Gwamnan PDP, Ya Bugi Kirji
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kalubalanci Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers kan siyasa
- Wike ya ce yana alfahari kan samar da gwamna dan kabilar Ijaw wanda Fubara bai isa yi shi kadai ba
- Tsohon gwamnan Rivers ya bayyana cewa shi bai goyon bayan ta da rigima ta kowane ɓangare inda ya ce suna bin doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya yi magana kan yadda ya samar da gwamna a jihar.
Wike ya ce ya yi alfahari kan yadda ya mayar da dan kabilar Ijaw zama gwamnan jihar Rivers.
Wike ya wanke kansa daga rikicin Rivers
Ministan ya bayyana haka ne yayin wani taro da dattawan kabilar Ijaw a yau Asabar 28 ga watan Satumbar 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce ba shi da wani nufi na tayar da rikici a jihar inda ya ce shi da magoya bayansa suna bin doka da oda.
Vanguard ta ruwaito cewa Wike ya caccaki Gwamna Siminalayi Fubara inda ya kalubalance shi kan wanda ya taba ginawa a siyasance tun da yake.
Rivers: Wike ya gorantawa Gwamna Sim Fubara
"Waye Fubara ya gina? duk abin da ka gani ana mana hassada mutane ba za su iya yi ba ne."
"Irin wadannan mutane su ne suke shan kaye a zabe, kuma a yanzu ma idan muka samu dama za mu kayar da su."
"Na samar da gwamna daga kabilar Ijaw, Ubangiji ya yi amfani da mu, dukkan mun sha wahala dalilin haka, waye yake son Ijaw fiye da wani?"
- Nyesom Wike
Wike ya nada hadimi na musamman
Kun ji cewa yayin da ake jita-jitar korar wasu Ministoci a gwamnatin Tinubu, Nyesom Wike ya nada hadimi na musamman a bangaren gudanarwa.
Ministan harkokin Abuja ya nada Dr. Samuel Atang a matsayin hadiminsa wanda ya taba rike shugaban gudanarwa a hukumar FCTA.
Wike ya kuma gargadi yan kwangila a birnin Abuja kan yawan samun jinkiri inda ya ce zai sallame su daga aiki inda ya yi musu barazanar kora.
Asali: Legit.ng