"Aljihunsu Kawai Suka Sani," Buba Galadima Ya Tona Asirin Ministoci da Hadiman Tinubu

"Aljihunsu Kawai Suka Sani," Buba Galadima Ya Tona Asirin Ministoci da Hadiman Tinubu

  • Buba Galadima ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin ministoci da hadiman da Bola Tinubu ya naɗa abin duniya suka tasa a gaba
  • Jigon jam'iyyar NNPP ya ce maimakon su maida hankali wajen gina ƙasa, tunaninsu ya karkata ne kan yadda za su cika aljihunsu
  • Buba ya koka kan ayyukan gwamnati mai ci a shekara ɗaya, inda ya nuna cewa ya yi tsammanin shugaban ƙasa zai taɓuka abin kirki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigon NNPP, Buba Galadima ya ce wasu daga cikin muƙarraban shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu aljihunsu kawai suka sani maimakon gina ƙasa.

Galadima ya bayyana cewa lokaci da ya yi da masu riƙe da muƙaman siyasa za su sauya tunaninsu daga abin duniya, kishin ƙasa ya zama shi ne abu na farko.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin garambawul, wani jigo ya yi magana kan ministocin da za a kora

Bola Tinubu da Buba Galadima.
Buba Galadima ya soki wasu muƙarraban Tinubu, ya ce kansu kadai suka sani Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buba Galadima
Asali: Getty Images

Buba Galadima ya yi wannan furucin ne da yake jawabi a shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba Galadima ya soki wasu mukarraban Tinubu

"Wasu daga cikin waɗanda aka naɗa a mukamai (a wannan gwamnatin) aljihunsu kawai suka sani, ba su tunanin yi wa kasa hidima.
"Babu wanda ke kishin gina ƙasa sai dai kishin aljihu, ya kamata ku san cewa shi shugaba abin misali ne," in ji Galadima.

Jigon NNPP ya ba da misali da ci gaban da ƙasar Indiya ta samu, yana mai cewa ƙasar wadda ke kudancin Asiya ta maida hankali ne kan kimiyya da fasahar sadarwa.

Galadima ya ba da misali da Indiya

"Da kuɗaɗen da ƴan Indiga da ke kasashen waje suka turo ƙasar suka bunƙasa ɓangaren fasaha da kimiyyar lafiya, a yau indiyawa ke jagotantar kaso 75% na duniya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga tsaka mai wuya kan korar Ministoci, an taso shi a gaba

"Ya kamata a faɗa masa (shugabaan kasa Bola Tinubu) cewa wasu daga cikin waɗanda ya naɗa kishin aljihunsu kawai suke yi, ba su damu da yi wa ƙasa aiki ba."

- Buba Galadima.

"Tinubu ya ba ni kunya" - Galadima

A wannan hira, Buba Galadima ya nuna damuwa game da ayyukan gwamnatin Bola Tinubu a shekara ɗaya da ta wuce, rahoton Daily Trust.

Ya ce ya yi tsammanin abubuwa da yawa daga Shugaba Tinubu bayan hawansa karagar mulki, amma shugaban ƙasar bai yi abin da ya dace ba.

Bola Tinubu ya naɗa daraktoci a NTA

A wani rahoton kuma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin manyan daraktoci bakwai a gidan taabijin na Najeriya (NTA).

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya sanar da haka ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262