NTA: Shugaba Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Naɗe 7 a Gwamnati, Sunaye Sun Bayyana
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin manyan daraktoci bakwai a gidan taabijin na Najeriya (NTA)
- Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya sanar da haka ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba
- Ya bayyana sunayen waɗanda aka naɗa da suka kunshi mutum ɗaya da aka sabunta naɗinsa da mutum shida da aka naɗa a karon farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sababbin daraktoci bakwai a gidan talabijin na Najeriya watau NTA.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a.
Channels tv ta ce a sanarwar mai taken, "Shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa manyan daraktoci bakwai a NTA," Onanuga ya jero sunayen nutanen da Allah ya ci da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen waɗanda Tinubu ya naɗa
Sanarwar ta bayyana cewa Bola Tinubu ya amince da sake naɗin Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA.
Punch ta tattaro sauran waɗanda aka naɗa sababbi sun haɗa da:
1. Ibrahim Aliyu (lauya masanin harkokin shari'a - Daraktan sashen ayyuka na musamman.
2. Muhammed Mustapha - Daraktan gudanarwa da horarwa.
3. Mis Apinke Effiong - Darakta a sashen harkokin Kudi.
Ta kasance kwararriya a harkar hada-hadar kudi tare da ajiya, haka kuma tana da gogewa a ɓangaren gudanarwa da dabarun bayar da rahoto.
4. Mis Tari Taylaur - Babbar darakta a sashen shirye-shirye.
5. Mista Sadique Omeiza - Babban daraktan sashen gyare-gyare.
6. Misis Oluwakemi Fashina - Daraktan sashen kasuwaci da tallace-tallace. Tana da kwarewa a ɓangaren kasuwanci da mu'amala.
Majalisa ta tabbatar da naɗin CJN
A wani labarin kuma mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta zama sabuwar shugabar alƙalan Najeriya watau CJN bayan tantancewa a majalisar dattawa.
Majalisar ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta tabbatar da naɗin a zamanta na ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng