Mutuwar Matar Gwamna: An Shiga Jimami, PDP Ta Dakatar da Yakin Neman Zabe

Mutuwar Matar Gwamna: An Shiga Jimami, PDP Ta Dakatar da Yakin Neman Zabe

  • Mutuwar mai dakin mai girma gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Eno ta jefa jihar cikin alhini da takaici
  • A sakon ta'aziyyarta ga gwamna Umo Eno, PDP a jihar ta yi addu'ar samun dangana ga iyalan marigayiyar
  • Jami'in hulda da jama'a na PDP a Akwa Ibom, Edwin Ebiese ya sanar da dakatar da yakin neman zaben da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit.Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Akwa Ibom - Mazauna Akwa Ibom sun wayi gari da labarin mutuwar matar gwamnan jihar, Patience Eno bayan rashin lafiya.

Lamarin ya kidima jama'a, wanda ya sa jam'iyyar PDP ta dakatar da gangamin yakin neman zabe da ta ke yi gabanin zaben kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga gidan gwamnati: Uwar gidan gwamna Eno ta rasu a asibiti

Patience
PDP ta yi alhinin mutuwar matar gwamnan Akwa Ibom Hoto: Pastor Patience Umo Eno
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Akwa Ibom a ranar 26 Oktoba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwa Ibom: Dalilin dakatar da yakin zaben PDP

Jaridar ta wallafa cewa a safiyar Juma'a ne jami'in hulda da jama'a na PDP a Akwa Ibom, Edwin Ebiese ya fitar da sanarwar dakatar da yakin neman zaben.

Ya ce mutuwar uwar gidan gwamna Umo Eno ya jefa su cikin bakin ciki, saboda haka aka dauki matakin dakatar da fita yawon neman kuri'ar mazauna jihar.

PDP ta ba jama'a hakuri a Akwa Ibom

Jam'iyyar PDP ta ba magoya bayanta da sauran yan jam'iyya hakuri saboda dakatar da yakin neman zaben kananan hukumomi da aka shirya yi a jihar.

Kakakin PDP na jihar Akwa Ibom, Edwin Ebiese ya nemi a taya gwamna Umo Eno alhinin wannan rashi, tare da addu'ar za su samu dangana a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

"An yi mana fashi da tsakar rana:" PDP ta soki sakamakon zaben gwamnan Edo

Mai dakin gwamnan Akwa Ibom ta mutu

A wani labarin , mun ruwaito cewa mai dakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Eno ta koma gidan gaskiya bayan ta sha fama fa rashin lafiya.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta nuna cewa Misis Patience Eno ta mutu a ranar Alhamis, 26 Satumba, 2024 kuma iyalanta na tare da ita a lokacin komawarta ga Mahalicci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.