‘Babu Gudu babu Ja da Baya’ APC Ta Fadi Yadda Za Ta Gwabza da NNPP a Zaben Kano

‘Babu Gudu babu Ja da Baya’ APC Ta Fadi Yadda Za Ta Gwabza da NNPP a Zaben Kano

  • Jami'yyar APC mai adawa ta fadi irin shirye shiryen da ta ke domin tunkarar zaben kananan hukumomi a jihar Kano
  • Shugaban APC a Kano ya ce sun shirya tsaf domin ka da kuri'a da kuma tabbatar da ba a sace musu kuri'a ko a yi maguɗi ba
  • Abdullahi Abbas ya yi kira na musamman ga hukumar zabe ta Kano kan yi musu adalci lokacin zaben da bayan tattara kuri'u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jam'iyyun siyasa na kara shiri yayin da zaben kananan hukumomi ke matsowa a jihar Kano.

Shugaban APC, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa jam'iyyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba domin tunkarar zaben.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

Ganduje
APC ta yi magana kan zaben Kano. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa APC ta ce za ta tabbatar ba a mata aringizon kuri'u ba a zaben da za a yi a ranar 24 ga Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta fara yakin neman zabe a Kano

Shugaban APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce a halin yanzu sun fara zaga gidaje da ƙauyuka domin zaburar da magoya bayansu.

Abdullahi Abbas ya ce hakan na cikin shirin da jam'iyyar APC ke yi wajen ganin ta lashe zaben a kananan hukumomi da dama.

APC za ta kare kuri'unta a zaben jihar Kano

The Guardian ta wallafa cewa APC a Kano ta ce za ta kasa, ta tsare a yayin zaben kananan hukumomi da zai gudana a watan Oktoba.

Abdullahi Abbas ya ce ba za su ji tsoron wata barazana ba, kuma za su dauki dukkan mataki da bai taka dokar kasa ba wajen ganin sun samu adalci.

Kara karanta wannan

Yiaga: Kungiya ta yi fallasa, ta zargi INEC da tafka maguɗi a zaben gwamnan Edo

Jam'iyyar APC ta yi kira ga hukumar zabe

APC ta bukaci hukumar zaben Kano ta yi mata adalci wanda ta ce hakan na cikin girmama dimokuraɗiyya.

Abbas ya ce Kano na cikin garuruwan da APC ke alfahari da su kuma za ta cigaba da rike jihar wajen samun nasara a lokacin zabuka.

Kotu ta yi hukunci kan zaben Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da jam'iyyun APC da PDP daga kawo cikas ga hukumar zaben jihar Kano (KANSIEC).

Kotun ta dakile jam'iyyun siyasa 21 daga hana hukumar karbar kudin fom na takara da ta gindaya tun farko kan zaben na kananan hukumomin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng