'Ka Yafe Mani Abin da ya Faru a Baya,' Gwamnan PDP ya Fadi Alakarsa da Tsohon Gwamna

'Ka Yafe Mani Abin da ya Faru a Baya,' Gwamnan PDP ya Fadi Alakarsa da Tsohon Gwamna

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce ba shi da wata matsala da tsohon gwamna, Rahidi Ladoja musamman a siyasance
  • Makinde ya ce tarihin siyasarsa ba za ta taɓa cika ba sai da saka hannun tsohon gwamnan watau Baba Rashidi Ladoja
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a gidan Ladoja da ke birnin Ibadan a Oyo yayin bikin murnar cikan dattijon shekaru 80

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya nemi yafiyar tsohon gwamna, Rashidi Ladoja.

Makinde ya nemi yafiyar ne bayan bambance-bambance da suke da shi da Otu Olubabadan a jihar.

Gwamna Makinde ya nemi yafiyar tsohon gwamna, Ladoja
Gwamna Seyi Makinde na Oyo ya nemi yafiyar tsohon gwamnan jihar, Rashidi Ladoja. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Twitter

Makinde ya yabi tsohon gwamnan Oyo

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya gaji da matsin lambar EFCC, ya roƙi Tinubu Alfarma

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron murnar cikan Ladoja shekaru 80 a duniya a gidansa da ke Ibadan, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya bayyana muhimmancin goyon baya da Ladoja ke ba shi a siyasance da tasirin hakan a gare shi.

Ya ce ba zai taba samun cigaba a siyasarsa ba da yanzu yake ciki ba tare da kokarin tsohon gwamna, Ladoja ba, Daily Post ta ruwaito.

Makinde ya nemi yafiyar tsohon gwamna, Ladoja

"Siyasata ba za ta yi tasiri ba, ba tare da gudunmawar Baba Ladoja ba wanda ya yi sanadin kasancewa ta gwamna a 2019."
"Tarihin siyasata ba za ta cika ba, ba tare da hannun Ladoja ba, ba ni da wata matsala da Baba."
"Watakila za mu iya samun matsala ko bambanci, ina mai rokonka ka yafe mani."
"Mu na godewa Allah da wannan rana da ta riske mu, tabbas abin farin ciki ne kuma ba zan gajiya da fada ba har yanzu akwai rawar da za taka a rayuwarmu."

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi yadda ya kwaci Dauda Lawal daga hannun EFCC, ya kalubalance shi

- Seyi Makinde

Oshiomhole ya roki gafarar Sarkin Benin

Kun ji cewa tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya roki basarake a jihar Edo kan kura-kurai da ya tafka lokacin yana gwamna.

Oshiomhole ya nemi afuwar Esama na birnin Benin, Gabriel Igbinedion inda yace ya dauki basaraken a matsayin uba a gare shi.

Sanatan ya fadi haka ne a jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 yayin taya basaraken murnar cika shekaru 90.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.