Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya kan Korar Ministoci, an Taso Shi a Gaba
- Yan siyasa da dama sun fara kama kafa tun bayan fitar da rahoto cewa Bola Tinubu ya shirya sallamar wasu ministocinsa
- Wasu daga cikinsu sun fara neman yadda za a yi yaransu su tsallake wannan sauye-sauye da za a yi a gwamnatin Tinubu
- Hakan ya biyo bayan samun labarin cewa shugaban zai yi garambawul domin kawo wasu sababbin jini a mukaman Ministoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirin garambawul a gwamnatinsa, yam siyasa sun fara zirga-zirga.
Tun bayan sanarwa kan garambawul din, wasu ke neman ganin shugaban kasar domin tabbatar da zaman yaransu a gwamnatin.
An taso Tinubu a gaba kan Ministoci
Wata majiya ta tabbatarwa Punch cewa manyan yan siyasa sun fara kama kafa domin ganin wadanda suka kawo ko yaransu sun tsallake.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce mafi yawansu sun kama kafa ne da na hannun daman Tinubu ciki har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Har ila yau, wasu Ministoci da kansu suke neman gindin zama a wurin wasu daga cikin na hannun daman Tinubu.
Yadda yan siyasa ke damun Bola Tinubu
"Tabbas haka ne, wasu daga cikin Ministocin sun kira iyayen gidansu a siyasa domin su yi musu wani abu."
"Wannan ba sabon abu ba ne a gwamnati, amma Tinubu zai yi abin da ya dace ne domin tabbatar da inganta kasa."
- Cewar majiyar
Har ila yau, wata majiya ta ce Gbajabiamila ya fara nuna damuwa yadda ake damun Tinubu kan mukaman Ministoci domin sanin makomarsu.
Majiyar ta ce saboda matsin lamba aka shawarci Tinubu ya wuce Burtaniya daga China domin ya samu sarari na yin tunani.
Tinubu ya yi magana kan korar Ministoci
Kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa nan ba da jomawa ba za a yi wa majalisar ministocin tarayya garambawul.
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba 25 ga Satumbar 2024.
Onanuga ya ce watakila a yi garambawul din kafin 1 ga watan Oktoba ko bayan hakan yayin da Tinubu ya yi kira ga ministocin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng